Wata sabuwa: Kamfanin NNPC ya musanta karin farashin man fetur, ya ce ba da yawunsa ba
- Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya musanta cewa shi ne ya kara farashin man fetur, inda ta ce ba laifsa ba ne kawo sabon farashi
- Kamfanin NPPC ya ce bai da masaniyar wani karin farashin man fetur kuma hakan ya zo ne a karkashin hukumar kula da harkokin man fetur ta NMPRA
- ‘Yan Najeriya dai sun firgita a ranar Talata lokacin da aka samu rahoton cewa NNPC ta kara farashin man fetur
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya, (NNPC) ya ce bai ba da izinin sabon jadawalin farashin man fetur ba da ke yawo a kasar.
A cewar kamfanin, farashin man fetur ya fito ne a karkashin kulawar hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya NMDPRA.
'Yan Najeriya sun kadu da sabon farashin man fetur
Garba Deen Muhammad, kakakin kamfanin na NNPC, ya bayyana cewa kamfanin ya daina kula da farashin man fetur.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma ce, NNPC ba ta da masaniya kan karin farashin, yana mai cewa hukumar NMDPRA ce ta amince da farashin man fetur ba NNPC ba.
Bangaren 'yan kasa kuwa, kowa ya shiga rudani a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, 2022 yayin da dillalan man fetur suka kara farashin mai daga N165 zuwa N179 kan kowace lita.
A binciken Legit.ng ta tattaro ya nuna cewa galibin ’yan kasuwa masu zaman kansu suna sayar da man fetur tsakanin Naira 170 zuwa 200 kan kowace lita wanda hakan ya saba wa umarnin gwamnatin tarayya.
NNPC ya kara farashin mai a gidajen mansa
A cewar Vanguard, 'yan kasuwa da dama na ci gaba da siyar da mai akan farashin da suka ga dama a yankuna daban-daban
Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano
Gidajen mai na kamfanin mai na kasa NNPC na sayar da man fetur a kan N169 a kan kowace lita a Legas yayin da manyan ‘yan kasuwa ke sayar da kan sama da N170 kan kowace lita.
Duk wannan karin a kan mu zai kare, ma'aikacin albashi
Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe ya ziyarci gidajen mai hudu shahararru a jihar a ranar Alhamis 21 ga watan Yuli domin duba ga farashin mai tare da jin ta bakin masu saye.
A gidan man AYM Shafa da ke Tumfure a hanyar Bauchi ta Gombe, ana sayar da man fetur a kan N210, hakazalika gidan man Shakkato da ke unguwar Manawachi shi ma farashinsu daya.
A gidan man Jiri Brothers, ana sayar da man akan N210, yayin da a Ummodah kuwa ake sayar dashi kan N220.
Wani malamin makaranta, Mallam Muhammad Hassan da wakilinmu ya zanta dashi yayin da ziyarci wani gidan man, ya shaida cewa, dole tasa yake sayen man kuma duk wani kari akan 'yan albashi yake karewa.
A cewarsa:
"Dole mu saya, kuma ko kadan babu dadi, amma dai ya fi mutum ya hau babur din haya ko keke napep.
"Mu dai ake cutarwa masu albashi, domin ba wanda zai kara maka albashi sai an kai ruwa rana, amma idan aka tashi kari, babu mai tunanin makomarka da ta 'ya'yanka.
Fatanmu Allah ya kawo mana dauki, amma shugabanninmu suna ba mu mamaki."
Shi kuwa Sani Ahmad Yahaya cewa ya yi:
"Mota nake dashi ta kai 'ya'ya na makaranta kafin na wuce aiki, amma yanzu babur nake hawa ta kani na na kai su kanina, saboda shagonmu daya. Idan ba gama hidimar yara, sai na dauke shi mu tafi shago.
"'Yan kasuwa kanana muna shan wahala, muma ai muna sayen abu a kasuwa. Idan muka tsauwala, to fa mu ma zamu je sayen kayan da bamu dashi, kai muna ma zuwa sari."
NNPC ta lallaba tayi karin farashin man fetur a fadin Najeriya, lita ya tashi daga N165
A tun farko, kamfanin mai na kasa watau NNPC Limited, ya amince da karin farashin litar fetur daga N165 da aka sani a gidajen mai zuwa akalla N179.
Rahoto ya fito daga The Guardian cewa karin da kamfanin NNPC suka yi zai fara aiki daga yau Talata, 19 ga watan Yuli 2022 a gidajen man kasar nan.
NNPC ya sanar da ‘yan kasuwa cewa su canza farashin da suke saidawa mutane litar man fetur. Ana sa ran daga yau sabon farashin zai fara aiki a ko ina.
Asali: Legit.ng