Lissafi ya Kwacewa Najeriya, Bashin da Ake Biya ya fi Karfin Kudin da Ake Samu

Lissafi ya Kwacewa Najeriya, Bashin da Ake Biya ya fi Karfin Kudin da Ake Samu

  • Gwamnatin Tarayya ta fitar da rahoton tattalin arziki na farkon shekarar nan, daga Junairu zuwa Afrilu
  • Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta ce biyan bashin da aka yi, ya fi kudin da aka samu
  • Zainab Ahmed ta ce tallafin man fetur zai ci kusan N7tr a shekara mai zuwa idan farashi bai tashi ba

Abuja - Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ankarar da Najeriya cewa bashin da gwamnati ke biya ya zarce kudin da ake samu.

This Day ta rahoto Ministar ta na cewa bashin da aka biya a farkon shekarar nan ta 2022 ya tsaya ne a kan N1.94tr, hakan har ya fi karfin kudin shiga da N310bn.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Bankin Duniya ya yi Mummunan Hasashe a kan Halin Najeriya

Zainab Ahmed ta kuma bayyana cewa an yi lissafin za a batar N6.72tr wajen biyan tallafin man fetur a 2023, idan aka cigaba da yi wa ‘yan Najeriya rangwame.

Kamar yadda The Guardian ta kawo wannan labari, Ministar duk ta yi wannan bayani ne wajen gabatar da dabarun tattalin arziki na MTEF-FSP a birnin Abuja.

Bashi ya tattara 40% na kudi

Ganin bashin da ke wuyan Najeriya ya yi yawa, Ministar kudi da kasafin kasar ta ce dole kwararru su kawo dabarun da ake bukata domin ceto tattalin arzikin kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga farkon shekarar bana zuwa karshen Afrilu, an kashe N4.72tr. Biyan bashi kadai sai da ya ci N1.94tr, abin da ya tafi wurin albashi da fansho shi ne N1.26tr.

Zainab Ahmed
Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ahmed ta ce N773.63bn sun tafi wajen yin ayyukan more rayuwa, alhali N1.63 kadai aka iya tatsa. Hakan na nufin bashi ya fi karfin kudin shiga da fiye da N300bn.

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

A cewar Ministar, Gwamnatin tarayya da Gwamnonin jihohi su na fuskantar kalubalen rashin kudi.

Kudin mai ya yi kasa a 2022

Rahoton da aka gabatar ya nuna daga cikin N3.12tr da aka sa ran za a samu daga mai da gas a farkon shekarar nan, N1.23tr kurum suka fito, ba a samu 40% ba.

Duk da danyen mai ya yi tsada a Duniya, Premium Times ta ce gwamnatin Najeriya ba ta samu kudi sosai a wannan lokaci ba saboda barnar masu fasa bututu.

Amma alkaluma sun nuna an samu karin kudin shiga ta fuskar sauran bangarori da fiye da 90%. Harajin VAT, CIT da kwastam sun karu a farkon shekarar nan.

Gyaran majalisa za ta ci N30bn

Dazu ne aka samu rahoto Gwamnatin Najeriya ta hakikance a kan ware fiye da Naira Biliyan 30 domin a gyara ginin majalisar tarayya duk da kukan babu kudi.

Kara karanta wannan

Mafi tsufa a raye: An gano wani tsoho dan Najeriya mai shekaru 126 a raye kuma da karfinsa

Ministan Abuja, Musa Mohammad Bello ya ce an fara wannan aiki, za a kammala a 2023. Mai girma Ministan ya bayyana haka ne a gaban kwamitin majalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel