NNPC ta lallaba tayi karin farashin man fetur a fadin Najeriya, lita ya tashi daga N165

NNPC ta lallaba tayi karin farashin man fetur a fadin Najeriya, lita ya tashi daga N165

  • Masu amfani da man fetur a Najeriya za su ga canji yayin da suka shiga gidajen mai daga yau
  • Babu wanda zai sake saida man fetur a kan N165, gwamnati ta amince da karin N4 zuwa N24
  • Kafin a canza farashin, mutane sun dade suna wahala kafin su iya samun fetur a gidajen mai

Abuja - Kamfanin mai na kasa watau NNPC Limited, ya amince da karin farashin litar fetur daga N165 da aka sani a gidajen mai zuwa akalla N179.

Rahoto ya fito daga The Guardian cewa karin da kamfanin NNPC suka yi zai fara aiki daga yau Talata, 19 ga watan Yuli 2022 a gidajen man kasar nan.

NNPC ya sanar da ‘yan kasuwa cewa su canza farashin da suke saidawa mutane litar man fetur. Ana sa ran daga yau sabon farashin zai fara aiki a ko ina.

Kara karanta wannan

Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida

Haka zalika kamfanin ya canza farashin da ake saida fetur a tashohin mai daga N148.17 zuwa N167. An samu kusan karin N10 kenan a kowace litar.

Farashi a kowane yanki

Kamar yadda mu ka samu labari, wannan karo sauyin farashin ya danganta ne da yanki. A kowane yankin kasar, akwai adadin kudin da NNPC ya kara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yankin Kudu maso yamma, daga N165, za a koma saida lita a kan N179, an samu karin N14. A Arewa maso yamma an yi karin N19 zuwa N184 kenan.

Man fetur
Ana zuba man fetur a mota Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Mutanen da ke zaune a Arewa maso gabas za su ga karin har N24 a duk lita. Daga yanzu za a koma saida litar man fetur a jihohin yankin a kan akalla N184.

Kamar karin da aka yi a Arewa maso yamma, ‘Yan Kudu maso kudu za su koma sayen fetur a N179, a kudu maso gabas, an ba gidajen mai damar kara N19.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Ni Zan Ci Zabe, In Ji Oyetola Bayan Ya Kada Kuri'arsa

Legit.ng ta na sane da cewa wannan sanarwar ta zo ne a lokacin da ake fama da wahalar fetur a kasa. A jihohi da-dama, an tara dogayen layi a gidajen mai.

A Legas ne inda aka yi mafi karancin karin na N4 rak, litar fetur ya can zai tashi daga N165 zuwa N169. Gidajen man da ke birnin tarayya kuwa za su yi karin N9.

Ana wannan yanayi ne wasu gidajen man suka bada sanarwar cewa sun canza farashin litarsu.

Sarki ya yi kira ga Buhari

Kun ji labari cewa Saƙon Abdulmumini Kabir Usman ga Muhamamadu Buhari shi ne a kammala manyan ayyukan cigaban da Gwamnatin Tarayya ta fara a jiharsa.

Mai martaba Sarki yana son ganin mutane sun amfana da gwamnati mai-ci wanda za ta sauka daga karagar iko a Mayun 2023 bayan shekaru takwas a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel