Bidiyon mai digirin digir yana tallar kwai a titi, ya nemi aiki sau 5000 bai samu ba

Bidiyon mai digirin digir yana tallar kwai a titi, ya nemi aiki sau 5000 bai samu ba

  • Dennis, wani dan kasar Kenya wanda ke da digirin digir ya koka kan yadda ya gaza samun aiki duk da kwalayen karatunsa
  • Dennis wanda yayi karatu a jami'ar Nairobi ya koma tallar kwai da miyar tumatir a titi domin samun na rufin asiri, yace sau 5000 yana neman aiki bai samu ba
  • Labarinsa ya taba zuciyar ma'abota amfani da soshiyal midiya inda wasu kuma basu yadda cewa yana da wannan ilimin ba ya kare a haka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Duk da mallakar digirin digir da yayi tare da sauran kwalayen shaida karatuttuka, wani 'dan kasar Kenya mai suna Dennis ya rasa aikin yi.

Bayan kammala digirinsa na farko a 2013, Dennis ya samu aiki amma ya yanke shawarar komawa karatu kuma yayi nasarar kammala digirinsa na biyu a 2018.

Mai tallar kwai
Bidiyon mai digirin digir yana tallar kwai a titi, ya nemi aiki sau 5000 bai samu ba. Hoto daga Afrimax English
Asali: UGC

Ya nemi aiki sau 5000 bai samu ba

Kara karanta wannan

Ci gaba: Dangote ya sake banke mutum 20, ya zama na 63 a jerin masu kudin duniya

Tun bayan da ya kammala digirinsa na biyu kuma ya tara kyawawan satifiket masu amfani, matashin wanda ke da shekaru 39 bai samu wani aikin ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin bada labarinsa a wani bidiyo mai taba zuciya da Afrimax English ta saka a YouTube, Deniis yace ya nemi aiki har sau 5000 amma bai taba samun ko daya ba.

Domin samu na rufin asiri, Dennis wanda ya karanci fannin tattalin arziki da kasuwanci ya koma siya da kwai danye, dafaffe da miyar tumatir a titin Nairobi.

Jama'a sun yi martani

Mildred Maponga yace: "A gaskiya wannan labari ne mai taba zuciya. Ya y abinda ya dace yayi. A gaskiya yana da zuciya kuma yanzu ne ma ya fara rayuwa a matsayinsa na matashi. Afrika ta saba yi wa jama'a irin haka. Wannan ne babban daliln da yasa ake ta tafiya wasu wurare domin samun abinci. Ubangiji na kallo kuma yanzu ya fara rayuwa. Mun gode."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya fadi abu 1 da zai bar wa ‘Ya ‘yansa gado idan ya bar Duniya

Nchilungbe Hiekha yace: "Lokacinsa ne bai yi ba. Zai yi arziki wata rana kuma zai zama maigidan kansa saboda shi kanshi ya wahala. Abubuwan alheri na daukan lokaci kafin su faru."

Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52

A wani labario na daban, fitacciyar jarumar masana'antar Nollywood, Bimbo Akinsanya wacce aurenta ya mutu lokacin tana da yaro mai wata uku a shekarun baya da suka gabata, tace ta mayar da hankali kan fim a yanzu fiye da batun aure.

A tattaunawarta da jaridar Vanguard, tace tana kokarin ganin ta bai wa 'danta lokacinta wanda hakan ke da matukar muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel