Ci gaba: Dangote ya sake banke mutum 20, ya zama na 63 a jerin masu kudin duniya

Ci gaba: Dangote ya sake banke mutum 20, ya zama na 63 a jerin masu kudin duniya

  • Dan Najeriya kuma mafi dukiya a Afrika ya sake tsallake matsayi mai girma a jerin attajiran duniya na Bloomberg
  • Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da Dangote ya tsallake wani matsayin mai ban mamaki a jerin
  • Rahoton da muka samo ya bayyana irin karin arzikin da Dangote ya samu har ya zama na 63 a duniya a yanzu

New York, Amurka - Attajirin Najeriya Aliko Dangote ya zama na 63 a jerin attajirai a duniya, kamar yadda wani sabon jadawali na Bloomberg ya nuna.

A cikin kididdigar da aka fitar jiya, shugaban Tesla, Elon Musk, ya fito a matsayin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya har ila yau, rahoton Vanguard.

Dangote, wanda ya haura matsayi 37 a jerin attajiran Bloomberg na baya-bayan nan, ya tara dala biliyan 20.2 ya zuwa ranar Litinin, 13 ga Yuli, 2022.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Mutumin da ya yi Hajjinsa a Kano ya magantu, ya bayyana dalilansa

Yadda Dangote ya zama na 63 a duniya
Ci gaba: Dangote ya banke mutum 20, ya zama na 63 a jerin masu kudin duniya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya kasance a matsayin mutum na 65 mafi arziki a duniya a ranar Juma'a 8 ga Yuli, 2022, kamar yadda rahoton mu na baya ya kawo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kididdigar biliniyoyi na Bloomberg wani kididdiga ne da ke auna kimar dukiyar attajiar a yau da kullum duba da tafiyar kasuwar hannayen jari.

Hakazalika, a kowace rana sabunta kiddigar ake kamar yadda kafar ta fada a wani rubutu da ta yi a baya-bayan nan

A cewar Bloomberg, kamar yadda Leadership ta kawo:

"An ba da cikakkun bayanai game da adadin na kididdigar ne da aka samo daga shafin bayanai na biliniyoyin. Ana kuma sabunta alkalumman a karshen kowace rana a New York."

Mu dawo ga Dangote, wanda ya fi kowa arziki a Afirka, sananne cewa yana kula da masana'antar Dangote, wacce ke samar da kusan komai na abubuwan rayuwar yau da kullum.

Kara karanta wannan

Manyan masu kudin Afrika 5, yawan arzikinsu da yadda suka tara dukiyarsu

Dangote ya mallaki 85% cikin 100% na masana'antar simintin Dangote da ke hannun jarin jama'a da dama.

Arzikin nufin Allah: Kudi sun karu, Dangote ya zama na 65 a jerin masu kudin duniya

A makon jiya, Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote, ya tsallake matsayi 35 a jerin attajiran duniya na Bloomberg, daya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, a cewar Bloomberg, yana da dala biliyan 20.4 kamar yadda a ranar Juma'a 8 ga Yuli, 2022, kuma hakan ne ya kai shi ga matsayi na 65 a mafi arziki a duniya.

Rahoton ya kuma nuna cewa daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa Yuli, Dangote ya samu dala biliyan 1.30, wanda hakan ya taimaka masa wajen barin matsayi na 100 da yake a farkon 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel