Shirin tsige shi: Mataimakin gwamnan Oyo ya maka majalisar dokoki a Kotu

Shirin tsige shi: Mataimakin gwamnan Oyo ya maka majalisar dokoki a Kotu

  • Mataimakin gwamnan jihar Oyo ya nufi babbar Kotun jiha da rokon ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga batun tsige shi
  • Majalisar ta fara shirin tsige shi daga muƙaminsa ne bayan sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, mambobi 24 cikin 34 suka amince da korafin
  • Suna zargin shi da aikata laifuka da suka haɗa da rashin ɗa'a da biyayya, kuma tuni ya kare kansa kamar yadda suka bukata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Injiniya Rauf Olaniyan, ya nufi babbar Kotun jiha da nufin ta dakatar da shirin tsige shi da majalisar dokokin jihar ke yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mambobi 24 cikin 32 na majalisar dokokin sun zargi mataimakin gwamnan, a cikin korafin, da, "Rashin ɗa'a, cin nutuncin Ofis, karkatar da kuɗi, rashin zuwa aiki, rashin biyayya da sauran su."

Mataimakin gwamnan Oyo, Rauf Olaniyan.
Shirin tsige shi: Mataimakin gwamnan Oyo ya maka majalisar dokoki a Kotu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa mataimakin gwamnan ya yi jawabi dalla-dalla kan dukkan zargin da majalisa ke masa ta bakin lauyan sa Afolabi Fashanu, SAN.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisa, Hon. Kazeem Olayanju, wanda ya tabbatar da haka, ya ce zasu ƙara tattauna wa kan lamarin ranar Laraba (wato yau).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lamarin ya bude sabon babi

Sai dai a ranar Talata, batun ya buɗe sabon shafi yayin da Olaniyan ya nufi Kotu tare da roko, bukatar Kotun ta yi wata doka da zata hana majalisa cigaba da bin matakan tsige shi.

Kotun ta ɗage zama kan karar da mataimakin gwamnan ya shigar gabanta zuwa ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.

Amma Kotun ta umarci kakakin majalisar dokokin ta jihar Oyo, Adebo Ogundoyin, da kuma magatakardan majalisa da su san da batun ƙarar.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa kujerar mataimakin gwamnan ta fara tangal-tangal ne tun bayan sauya shekar da ya yi daga PDP zuwa APC.

A wani labarin kuma Alƙalin Kotun Musulunci ya ɗage shari'ar jaruma Hadiza Gabon saboda matarsa bata da lafiya

Alƙalin Kotun Shari'ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna, Khadi Rilwanu Kyaudai, ya ɗage cigaba da zaman shari'ar fitacciyar jarumar Kannywood , Hadiza Gabon.

An ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 1 ga watan Agusta, 2022, biyo bayan rashin lafiyar da matar Alƙalin ke fama da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel