Yanzu-yanzu : Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Jihar Filato

Yanzu-yanzu : Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Jihar Filato

  • Wasu ‘yan bindiga sun yi wa tawagar sojoji kwanton bauna a kauyen Zurak Kampani da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato
  • Rundunar Sojin Najeriya ta ce yan bindiga ba su samu nasarar kashe musu jami'i ko guda ba yayin da suka dakile harin
  • Mutanen karamar hukumar Wase na jihar Filato na fama da matsalar yan fashi wanda ya tilasta wa da yawa barin gidajensu.

Jihar Filato - Wasu ‘yan bindiga sun yi wa tawagar sojoji kwanton bauna a kauyen Zurak Kampani da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato. Rahoton Daily Trust

‘Yan bindigar, a cewar mazauna yankin, sun isa unguwar ne a lokacin da mazauna yankin ke gudanar da harkokin kasuwa.

Al'ummar Zurak Kampani sun haura kilomita 100 daga hedkwatar karamar hukumar.

armyn
Yanzu-yanzu : Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Jihar Filato FOTO VANGUARD
Asali: Facebook

Manjo Ishaku Takwa, mai magana da yawun rundunar tsaro da dama, Operation Safe Haven (OPSH) mai wanzar da zaman lafiya a jihar, ya tabbatar da harin na kwanton bauna amma ya ce babu wani soja da ya rasa ransa rayuwar sa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Kotu ta daure janar din soja na bogi shekaru 7 a magarkama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wani mazaunin garin Wase Abdullahi Usman ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun kashe soja daya tare da raunata daya.

Ya ce sojojin da ke yankin sun dakile harin.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa kwana guda kafin harin kwantan bauna, ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Pinau na karamar hukumar, inda suka yi awon gaba da shanu sama da 500.

Al’ummar Wase na fama da matsalar ‘yan fashi a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya tilasta wa da yawa barin gidajensu.

Zaben Osun: Muna sa ido kan abubuwan da ke faruwa – EFCC

A wani labari, Wasu jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, sun ce suna lura da yadda abubuwa ke gudana a zaben gwamnan jihar Osun. Rahoton PUNCH

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani malamin addini a Adamawa, sun kuma yi awon gaba da diyarsa

EFCC na cikin jami'an tsaron da aka tura jihar Osun domin sa ido akan yadda zaben ke gudana dan dakile musa saye da siyar da kuri'u.

Asali: Legit.ng

Online view pixel