Saura kiris yajin aikin ASUU ya zo karshe, FG ta bayar da tabbaci

Saura kiris yajin aikin ASUU ya zo karshe, FG ta bayar da tabbaci

  • Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na aiki ba ji babu gani don ganin yajin aikin ASUU ya zo karshe
  • Wannan shine tabbacin da karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah, ya baiwa manema labarai a garin Owerri
  • Ya kuma tabbatar da cewar nan ba da jimawa ba dalibai za su koma ajujuwansu domin ci gaba da karatu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Imo - Karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin kawo karshen yajin aikin malaman jami’a (ASUU) nan bada jimawa ba.

Ministan ya bayar da tabbacin ne a Owerri, babban birnin jihar Imo a karshen mako yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a yayin wani liyafa da abokansa suka shirya masa.

Ya ce:

“Zan iya tabbatar maku cewa gwamnati ta damu sosai game da lamarin. Har yanzu da nake magana da ku tunane-tunane da dama, tattaunawa da dama da taruka na gudana da nufin magance lamarin cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

Dukan Fasinjojin Jirgin Kasa: Duk Munafukai Ne Masu Allah Wadai A Soshiyal Midiya, Naziru Sarkin Waka

Buhari
Saura kiris yajin aikin ASUU ya zo karshe, FG ta bayar da tabbaci Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana fatansa cewa za a kawo karshen rashin jituwa nan ba da jimawa ba, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya kara da cewa:

“Ina kyautata zaton cewa za a magance rashin jituwar da ke tsakanin gwamnati da malaman ASUU nan ba da jimawa ba domin yaranmu su koma makaranta.”

Ministan ya ce matsalolin da ke ma’aikatar ilimi na da wuyar gaske kuma gwamnatin tarayya bata yi kasa a gwiwa ba wajen neman mafita da kawo karshen yajin aikin kungiyar ASUU.

Ya ce a shirye yake ya bayar da gagarumin gudunmawa a ma’aikatar ta hanyar aiki tare da ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, rahoton The Cable.

Ya ce:

“A shirye nake na bayar da gudunmawa a ma’aikatar da bangaren ilimi ta hanyar aiki tare da ministan, Mallam Adamu Adamu. A duk inda matsaloli suke dole akwai mafita. Kuma ina iya tabbatar maku cewa za mu nemo mafita kuma yaranmu za su koma makaranta.”

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

legit Hausa ta zanta da wani dalibi da ke karatu a jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato mai suna Jabir Abubakar, inda ya nuna farin ciki da wannan tabbaci na karamin ministan ilimi.

Abubakar ya ce sun fara gajiya da gafarar sa ba kaho a kan wannan lamari na yajin aikin ASUU da ya ki ci ya ki cinyewa.

Ya ce:

“Alhamdulillah Gaskiya Munji Dadin Wannan kalamin da karamin ministan ilimi yayi a Jahar Imo, Nacewa gwamnati nan Na neman Sasantawa da kungiyar malaman jami'oi Kan yajin aikin Asuu, Wanda Kowa yasani gaskiya Mu Daliban Nijeriya mun gaji da jin gafara sa Bamu ga kaho ba.
“Amma muna Fatan Wannan kalamin Da karamin ministan ilimi yayi da abin Shugaba Buhari yace yayi sanadiyyar kawo Mana karshen Wannan yajin aikin da Muke Ciki Ameen”

Wata lakcara a jami’ar FUT Minna da ta nemi a sakaya sunanta ta ce lallai ko su suna ji a jikinsu domin basa samun albashi ga kuma harkoki sun tsaya cak, amma duk da haka tace gwara a kwato masu yanci daga wajen gwamnati.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku ya bayyana matsayarsa ta yin sulhu da gwamnan PDP Wike

Ta ce:

“Muma ba a son ranmu ne muke yajin aiki ba amma gwamnati ce ta ki bayar da hadin kai ta yadda kowani bangare zai samu salama.
“Ko mu yanzu haka muna ji a jikinmu don albashi baya shiga ga harkoki amma duk wadannan sadaukarwar muna yi ne domin tsarin jami’ar kasar nan ta gyaru. Samun maslaha shine abun da muma muke fata."

A Shirye Muke Mu Janye Yajin Aiki, In Ji 'Kungiyar ASUU

A gefe guda, kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, ta ce a shirye ta ke ta janye yajin aikin game gari da ta ke yi a kasar, rahoton Daily Trust.

ASUU ta fara yajin aikin gargadin ne domin janyo hankali kan bukatunta, tun a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Daga bisani kungiyar ta ayyana cikakken yajin aiki, tana zargin Gwamnatin Tarayya da rashin gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel