Yadda ‘Yan ta’adda suka kula da mu inji Fasinjan Jirgin Abuja-Kaduna da ya kubuta

Yadda ‘Yan ta’adda suka kula da mu inji Fasinjan Jirgin Abuja-Kaduna da ya kubuta

  • Sababbin bayanai na fitowa game da tare jirgin kasa a Kaduna da fasa gidan yari da aka yi a Abuja
  • Wani a cikin Fasinjojin da yanzu ya samu ‘yanci ya ce Boko Haram sun hada-kai ne da ‘Yan bindiga
  • Da taimakon ‘Yan bindiga aka kai wa jirgin Abuja-Kaduna hari, kuma aka boye fasinjojin cikin jeji

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Wani daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka saki ya bada labarin halin da ya samu kan shi, su ne fasinjojin jirgin kasan da aka tare a hanyar Abuja.

Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto ranar Litinin, wannan mutum ya ce akwai hadin-kai tsakanin ‘Yan Boko Haram da ‘yan bindigan da suka dauke su.

“Su (Boko Haram) shiga yarjejeniya da ‘yan bindiga domin su amfana da yawan sojojinsu da kuma sanin da suka yi wa jirgin kasan.”

Kara karanta wannan

Yanzun nan: An yi ram da daya daga cikin wadanda suka tsere daga kurkukun Kuje

“Har jejin da suka ajiye mu a kusa da Birnin Gwari, ba yankinsu ba ne, sun fada mana sai da suka nemi umarnin ‘yan bindigan yankin.”

- Fasinjan da aka dauka

Majiyar ta shaidawa jaridar a boye cewa a budadden wuri aka ajiye su, babu komai sai bukkoki uku. Maza suka raba biyu, mata da yara su ka rabe a cikin guda.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda yake fada, wannan fasinja ya ce su 20 ne a tsare, amma ba a muzanta masu ba, a cewarsa sau daya aka taba yi masu duka – ranar da aka kawo su.

Jirgin Abuja-Kaduna
Lokacin da aka kai wa jirgin kasa hari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Har da cin nama a jeji

“Wasu ranakunan za su yanka mana Saniya. Na karshe shi ne wanda suka yanka domin murnar bikin sallah.”
“Kuma su kan yi mana wa’azi da kan su, ko kuma mu saurari wa’azin wasu fitattun malamai da aka dauka.”

Kara karanta wannan

Yadda ‘Yanuwa suka biya N800m kafin su ceto Fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Fasa Gidan yarin Kuje

Wannan majiya ta iya tabbatar da cewa wadanda suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja ne suka dura gidan gyaran hali na Kuje a Abuja.

Mutumin da ya kubuta yake cewa ‘yan ta’addan sun yi ta murna a daren da aka fasa kurkukun, wanda a dalilin haka ‘Yan Boko Haram akalla 69 suka sulale.

A wani faifen bidiyo da aka fitar, an tabbatar da cewa ‘Yan kungiyar ISWAP ne suka yi wannan aiki. ‘Yan ta’addan ne ake zargin sun tare jirgin kasa yana tafiya.

An biya N800m

Kun ji Daloli da makudan miliyoyi sun yi aiki kafin a saki mutum bakwai cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja da miyagun ‘yan ta’adda suka dauke a watan Maris.

‘Yanuwan Muhammad Paki, Bosede Olurotimi, Abubakar Zubairu, Alhassan Sule, Sadiq Ango, Aliyu Usman sun biya N600m, iyalin Abuzar Afzal sun bada N200m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel