'Yar shekara 19 ta gwangwaje mijinta da dalleliya motar N87m, karo 3 da mata suka yi bajinta

'Yar shekara 19 ta gwangwaje mijinta da dalleliya motar N87m, karo 3 da mata suka yi bajinta

  • Cikin kwanakin nan, mata da dama sun nuna bajimtarsu wajen ba wa mazajensu kyautar motocin alfarma
  • Hakan bai sha bamban da wata mata 'yar shekara 19 mai juna biyu da ta gwangwaje mijinta da kyautar mota kirar Lamborghini mai kimar N87 miliyan
  • A al'adarta, miji ne ke da alhakin rainon jinjiri idan mata ta haihu har sai ta dawo daga gida wanka, inda hakan ya zama dalilin masa kyautar don yaba wa da aikin da zai yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kafin yanzu, maza ne aka fi sani da da dabi'ar ba wa matansu, 'yan matansu da wadanda zasu aura kyautar motoci a matsayin ba-zata kafin wasu mata su canza salon kidan. Wasu mata da suka bawa mazajensu da suke matukar kauna kyautar sabbin motoci.

Legit.ng sun sake bibiyar labarai uku da suka yadu na wasu mata da suka gwangwaje masoyansu da kyautar mota.

Kara karanta wannan

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

Masoyan juna
'Yar shekara 19 ta gwangwaje mijinta da dalleliya motar N87m, karo 3 da mata suka yi bajinta. Hoto daga Adeyemi Holubunmy Crown, TikTok/@ayunieso24, @reigndolll
Asali: Facebook

1. Wata mata 'yar Najeriya ta gwangwaje masoyinta da sabuwar mota a ranar zagayowar aurensu a watan Satumban 2021, matar 'yar Najeriya ta tada kura a shafukan sada zumuntar zamani bayan tayi wa mijinta kyautar ba-zata a sabuwar mota.

Matar mai suna Adeyemi Holubunmy Crown ta mallaka wa mijinta sabuwar motar ne a ranar zagayowar shekarar aurensu na bakwai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da ta damka masa mukullin motar, matar ta rubuta a shafinta na Facebook:

"Wannan kadan ne daga cikin irin kaunar da nake maka. Ina matukar kaunarka kuna babu abun da zai canza hakan. Crown Kay Amos kafi kowa."

An ga yadda mijinta Crown Kay Amos ke murmushi a hotunan yayin da ya amsa kyautar motar daga rabin ransa.

2. Budurwar da ta ba saurayinta kyautar dalleliyar mota kirar Range Rover

Kara karanta wannan

2023: PDP ta yi dabara, ta zabo wanda zai kawo karshen APC a Gombe, inji tsagin dan takara

Wata budurwa ta gwangwaje saurayinta da kyautar ban mamaki da sabuwar mota kirar Range Rover.

Budurwar cikin tsananin farinciki ta wallafa bidiyon lokacin da ta damka masa kyautar a shafin sada zumuntar zamani, wanda ya ja masu amfani da yanar gizo da dama tofa albarkacin bakinsu.

Yayin da mutane da dama suka yi mamakin irin karamcin ta, sai dai da damarsu sun lura da yadda sauranyin nata bai wani yaba da kyautar ba.

An lura da hakan a bidiyon, inda ko godiya bai mata ha ko nuna tabawa ta hanyar sumbatarta ko rungumarta.

3. Wata mata mai juna biyu ta gwangwaje mijinta da motar N87 miliyan cikin watan Maris, matar mai shekaru 19 ta matukar ba wa masu amfani da yanar gizo mamaki da kyautar da ta wa mijinta.

Matar mai suna Anes Ayuni Osmanis ta mallaka masa sabuwar mota kirar Lamborghini Huracan Evo wacce ta kai kimar N87 miliyan gami da wallafa bidiyon lokacin da ta kai shi wajen siyar da motocin inda aka bude sabuwar motar.

Kara karanta wannan

Bayan kama matar aure dumu-dumu da gardi, an tilasta mata zagaya kauye da mijinta a kafadarta

A al'adarta, ana sa ran mijin ne zai kula da jinjirin idan an haifesa har sai ta dawo daga gida wanka.

Kyautar motar da matar 'yar Malaysia tayi hanya ce na saka wa masoyinta rainon jinjirin da zai yi wanda ya zama masa wajibi.

Mijinta ya yi matukar farinciki a bidiyon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel