Bayan kama matar aure dumu-dumu da gardi, an tilasta mata zagaya kauye da mijinta a kafadarta

Bayan kama matar aure dumu-dumu da gardi, an tilasta mata zagaya kauye da mijinta a kafadarta

  • Mazauna kauyen Borpadaw dake Indiya sun tilasta wata matar aure yawo da mijinta a kafadarta har ta zagaye dukkan kauyen
  • Hakan ya faru ne bayan an kama matar a dakin gardi bayan kwashe mako daya da mijinta yayi da sirikanta suna nemanta
  • Bayan ta dauke shi a kafadar ta zagaye kauyen, ya sagala mata takalmansa a wuyanta inda suka zagaye kauyen yana nuna ta

An tirsasa wata matar aure ta dauka mijinta a kafadunta kuma ta zagaye titunan kauyensu bayan an kama ta dumu-dumu da wani gardi.

Shafin LIB ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Borpadaw aake Indiya a ranar 3 ga watan Yulin 2022.

Matar aure dauke da mijinta
Bayan kama matar aure dumu-dumu da gardi, an tilasta mata zagaya kauye da mijinta a kafadarta. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Matar tayi batan-dabo na tsawon sati kuma mijinta da sirikanta sun dinga nemanta amma basu ganta ba.

Kara karanta wannan

Matar Marigayi Alaafin Na Oyo Ta Dawo Daga Saudiyya Kawai Sai Ta Tarar Da Kyautar Mota Daga Wani Bawan Allah

Daga bisani sai mijin ya yanke shawarar mika rahoton batan matarsa kuma a lokacin ne wani yazo ya sanar da jami'ai cewa ta tare ne a gidan saurayinta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An zargi cewa mijin matar ya zane ta, ya ja mata gashin kanta kuma ya buga ta da kansa bayan ya gane cewa tana mu'amala da wani namiji.

Daga nan ne aka sa ta dole ta dauke shi tare da zagayawa dashi kauyen.

A hotunan da suka bayyana, an gan ta dauke da mijin a wuyanta da kafadunta yayin da take tattakawa zuwa titunan kauyen kuma jama'a na biye da ita.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, daga nan mijin ya cigaba da yawo da ita suna zagaya kauyen yayin da ya sagale takalmansa a wuyanta.

A halin yanzu, an cafke mutum tara masu hannu a lamarin kuma an tura ta gidan iyayenta.

Kara karanta wannan

Matar Aure Tayi Hayar Macen Da Za Ta Dinga Gamsar Da Mijinta, Ta Saka Mata Albashin N145K Duk Wata

Bidiyon auren basarake da kada, ya sumbaceta cike da kauna a kayataccen bikin

A wani labari na daban, ko kana tunanin ka gama ji da ganin abun al'ajabi? To ga labarin wani Sarki a Mexico da ya auri Kada wanda zai daure maka kai.

Rahotanni sun bayyana yadda Sarkin, Victor Hugo Sosa na kauyen Pedro Humelula ya auri kada da ke sanye da rigar aure tare da kulla alakar aure ta hanyar sumbatarta cike da soyayya.

An gano yadda shagalin bikin ya kasance wani bangare na al'ada don kawo yalwa ga kauyen kudu maso yammacin Mexico.

Asali: Legit.ng

Online view pixel