Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta Umarci a cigaba da tsare Sanata Ekweremadu da matarsa

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta Umarci a cigaba da tsare Sanata Ekweremadu da matarsa

  • A yau Alhamis, Sanata Ike Ekweremadu, da matarsa sun gurfana a gaban Kotun Majistire ta ƙasar Birtaniya kan zargin yanke sassan jiki
  • Bayan tafka muhawarawa tsakanin ɓangarori biyu, Kotu ta yanke cewa wanda ake shari'ar kansa, shekarunsa 21 ba 15 bane
  • Ta kuma ɗage zaman zuwa 4 ga watan Agusta, 2022 kuma ta maida Kes ɗin Kotun manyan laifuka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

UK - Kotu ta ɗage zaman shari'ar tsohon mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, da matarsa, Beatrice zuwa ranar 4 ga watan Agusta, 2022.

An sake gurfanar da ma'auratan a gaban Kotun Majistire Westminster bisa tuhumar yanke sassan jikin mutum ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gavin Irwin, shi ne lauya mai kare Sanata Ekweremadu, yayin da Szilvia Booker, ke wakiltar mai ɗakinsa.

Kara karanta wannan

Valentine Day: Matashin saurayin da ya kashe budurwarsa ranar masoya zai baƙunci lahira a Jos

Kotun da ake shari'ar Ekweremadu a Birtaniya.
Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta Umarci a cigaba da tsare Sanata Ekweremadu da matarsa Hoto: thecableng
Asali: UGC

Manyan jiga-jigai a Najeriya sun halarci zaman Kotun na yau don sauraron shari'ar da ake wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗan da suka halarci zaman sune; tsohon shugaban majalisa, David Mark, tsohon shugaban marasa rinjaye, Eyinnanya Abaribe, tsohon ƙaramin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, da kuma shugaban kwamitin harkokin waje na Sanatoci, Adamu Bulkachuwa.

Yadda zaman Kotun ya kasance

Tun da farko, Luayan sanata ya musanta duk wata tuhumar amfana a Kes ɗin, "Mun musanta duk wani kalar amfana ko yunkurin hakan a gaba," a cewar lauyan yayin da yake jawabin buɗe wa.

A zaman shari'ar lauyoyin da ke kare waɗan da ake ƙara sun yi musun cewa mutumin da abun ya shafa ƙaryar shekaru ya yi, yayin da masu ƙara suka tsaya kan bakarsu cewa yaro ne ƙarami.

Alkalin ya yanke cewa, wanda ake tafka muhawara kansa, David Okpo, kotu ba zata sake kallon shi a matsayin yaro ba, a cewar Kotun shekarun Okpo 21 ba 15 ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai wa Ayarin motocin shugaba Buhari hari a Katsina, sun jikkata mutane

The Nation ta ruwaito cewa Sanata Ekweremadu da matarsa sun bayyyana a zaman yau Alhamis kuma sun musanta tuhumar da ake musu na yanke sassan jiki.

Kazalika an maida Kes ɗin Kotun manyan laifuka, kana aka umarci a cigaba da tsare waɗan da ake zargi har zuwa 4 ga watan Agusta.

A wani labarin kuma jirgin yaƙin NAF ya yi luguden wuta kan yan bindiga bayan kai wa Ayarin Buhari hari a Katsina

Bayan harin da yan bindiga suka kai wa Ayarin shugaba Buhari, jirgin yaƙin NAF ya yi luguden wuta kan tawagar yan bindiga har biyu a Katsina.

Bayanai da suka biyo bayan samamen na sama sun nuna cewa jirgin ya hallaka aƙalla yan ta'adda 42 a kauyukan ƙaramar hukumar Safana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel