Kotu ta yanke wa matashin da ya kashe budurwarsa hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke wa matashin da ya kashe budurwarsa hukuncin kisa ta hanyar rataya

  • Babbar Kotun jihar Filato da ke zamanta a Jos ta yanke wa wani saurayi hukuncin kisa ta hanyar taya bisa kashe budurwarsa
  • Alkalin Kotun, Mai shari'a Arum Ashom, ya ce Hujjojin da aka baje masa a gaban Kotu sun tabbatar da laifin wanda ake zargi
  • An gurfanar da matashin ɗan shekara 35, David Dele, kan tuhumar kashe masoyiyarsa a ranar Masoya ta duniya a 2016

Jos, Plateau - Matashin saurayi ɗan shekara 35 a duniya, Badung David Dele, wanda ya yi ajalin budurwarsa ranar masoya ta duniya a shekarar 2016, zai baƙunci lahira ta hanyar rataya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Alƙalin babbar Kotun Jos, mai shari'a Arum Ashom, shi ne ya yanke wa suarayin hukuncin kisa ranar Talata.

Za'a rataye wani matashi a Jos kan kisan budurwarsa.
Kotu ta yanke wa matashin da ya kashe budurwarsa hukuncin kisa ta hanyar rataya Hoto: punchng
Asali: Twitter

Mai Shari'a Ashom ya ce Kotu ta kama wanda ake zargin da aikata laifin kisan kai wanda ke ɗauke da hukuncin kisa ƙarƙashin sashi na 221 a Fenal Code, Cap 89 a kundin dokokin arewacin Najeriya 1963.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sa'kai sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga a Filato, rayuka sama da 10 sun baƙunci lahira

Naija Cover ta rahoto cewa Da yake yanke hukunci yayin zaman Shari'ar, Alkalin Kotun ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Lauyoyi masu shigar da kara sun sauke nauyin da ke kansu game da wanda ake zargi ta hanyar gamsar da Kotu cewa ya aikata laifin fiye da kokwanto."
"Wanda ake tuhuma ya gaza kare kansa kan laifin kuma Kotu ta gamsu da ƙwararan hujjojin da masu ƙara suka baje mata cewa wanda suke tuhuma ne ke da alhakin mutuwar Nanchin Zakaria a watan Fabrairu, 2016."
"Duba da Hujjojin da ke gaban Kotu, mutumin da ake zargi ya aikata laifin dumu-dumu kuma bisa haka Kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Muna fatan Allah ya yi masa rahama."

A wani labarin kuma 'Yan Sa'kai sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga a Filato, rayuka sama da 10 sun baƙunci lahira

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

Akalla mutane 12 ake fargabar sun rasa rayukansu a wata arangama tsakanin Yan Bijilanti da miyagun yan bindiga a ƙauyen Zak, ƙaramar hukumar Wase, jihar Filato.

Wani shugaban matasa a yankin Wase, Shapi'i, wanda ya tabbatar da lamarin, ya shaida wa wakilin jaridar Leadership cewa lamarin ya auku ne da ƙarfe 9:00 na safiyar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel