'Yan bindiga sun kwace asibitoci 72 a jihar Katsina, Gwamna Masari

'Yan bindiga sun kwace asibitoci 72 a jihar Katsina, Gwamna Masari

  • Gwamnatin jihar Katsina ta garkame kananan asibitoci 72 da ke kananan hukumomin jihar saboda yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka
  • Sakataran kungiyar bunkasa kananan asibitoci, Dr Shamsuddeen Yahaya ya bayyana Jibia, Safana, Batsari, Sabuwa, Faskari da sauransu a matsayin inda hakan ya shafa
  • Ya kara da bayyana yadda matsalar tsaro tayi matukar shafar harkar lafiya a jihar, tare da labarta yadda 'yan bindiga suka kona kananan asibitoci 2 da ba a dade da gyarawa ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta garkame a kalla kananan asibitoci 72 a kananan hukumomin jihar bisa munanan ayyukan 'yan ta'adda, PM News ta ruwaito.

Sakataran kungiyar kananan cibiyoyin lafiyar jihar, Dr. Shamsuddeen Yahaya, ya bayyana hakan a ranar Talata a wata tattaunawa da manema labarai a Katsina.

Kara karanta wannan

Buhari ya sake nada Hajiya Saratu Umar a matsayin shugabar hukumar NIPC

Gwamnan Katsina
'Yan bindiga sun kwace asibitoci 72 a jihar Katsina, Gwamna Masari. Hoto daga pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce, kananan asibitoci da hakan ya shafa su na wurare daban-daban na yankunan da ke matukar wuyar riska a Jibia, Safana, Batsari, Faskari, Sabuwa da sauran kananan hukumomin jihar.

Ya kara da cewa, 'yan ta'adda sun kona kananan cibiyoyin lafiya biyu da ba a dade da gyarasu ba a karamar hukumar Batsari, inda ya ce rashin tsaro matukar shafar harkar lafiya a jihar.

A cewarsa: "Wasu daga cikin asibitoci musamman a wadannan kananan hukumomin na da kalubalen. Misali, mun gyara cibiyoyin lafiya biyu a Batsari amma 'yan bindiga sun kai farmaki gami da kona su.
"A halin yanzu, an garkame kimanin cibiyoyin lafiya 72 a Jibia, Safana, Batsari, Sabuwa, Faskari da sauran kananan hukumomin saboda matsalar rashin tsaro sannan an yi garkuwa da wasu daga cikin ma'aikatanmu daga bisani aka sake su.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

"Wani kalubale shi ne yadda duk mako muke samun shigar da bukatu daga ma'aikatanmu, musamman mata, kan cewa suna son a dauke su daga anguwanni zuwa ko dai Katsina, Batagarawa ko Kaita. Wadannan ne matsalolin da muke fama dasu."

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya kara da cewa gwamanatin jiha ta shirya daukar sabbin ma'aikata 272 don magance matsalar da ke addabar harkar lafiya a jihar.

Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

A wani labari na daban, a kalla rayuka 17 sun salwanta bayan wadanda suka samu matsanantan raunuka yayin da 'yan ta'adda suka kai farmaki mahakar ma'adanan da 'yan kasar Sin ke kula dashi tsakanin Ajata da Aboki cikin gundumar Gurmana na karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

An ruwaito yadda harin ya auku ranar Laraba da tsakar rana inda aka halaka mutane 17 duk da 'yan sandan da ke tsere mahaka ma'adanan da ma'aikata.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Hotuna sun nuna lokacin da Tinubu ke matashi, ya halarci jami'a a Turai

An gano yadda maharan suka yi dirar mikiya da miyagun makamai misalin karfe 2:00 na rana a anguwar, inda suka doshi wajan da ake hakin tare da budewa duk wanda suka yi tozali dashi wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel