Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

  • Yan daba sun kai farmaki wajen taron matasan jam’iyyar PDP Ologba da ke karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi
  • Lamarin ya haifar da tashin hankali da fargaba a yankin, inda aka yi asarar dukiya da ababen hawa
  • Sai dai kuma har yanzu ba a ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, SP William Ovye Aya, game da lamarin ba domin baya amsa kiran waya

Kogi - Akalla mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 10 ne suka jikkata a garin Ologba da ke karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi bayan wasu yan daba sun farmaki wajen taronsu.

Wani ganau ya ce an yi amfani da bindigogi, wukake da sauran makamai a arangamar yayin da maharan suka kona gidaje, babura da motoci, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jihar Kogi
Mutane da dama sun jikkata, an kona dukiya yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi Hoto: Daily Post
Asali: Twitter

Wani dan PDP, Ajibili Eshu ya ce:

Kara karanta wannan

Yan Daba Sun Tarwatsa Taron PDP, Sun Raunata Mambobi Sun Kona Motocci Da Babura A Jihar Arewa

“Hankula sun yi matukar tashi a karamar hukumar Dekina. Yan daba sun je wajen taron matasan PDP a ranar Lahadi a Ologba, sun lalata dukiyoyi, sun kona babura da motoci.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin da ake ciki, wata kungiya karkashin inuwar Igala Vanguard ta yi Allah wadai da harin sannan ta bukaci a gaggauta kama wasu mutane.

Kakakin kungiyar, Mista Akpa Ocheni, ya yi kira ga jami’an tsaro da su kama su kan zargin jagorantar wani harin siyasa kan jam’iyyar adawa.

Ya ce:

“Igala Vanguard ba za ta yarda da siyasar rikici ba a wannan karon kuma duk za a zuba ido don ganin cewa an hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asar.”

Sai dai kuma, duk wani kokari na jin ta bakin kakakin yan sandan jihar, SP William Ovye Aya, game da lamarin ya ci tura, domin baya amsa kiran waya, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga, ya bayyana halin da ya shiga

Shugaban APC na shiyyar wata jiha da dubba mambobin sun koma PDP

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Bashiru Ajibade, ya jagoranci daruruwan ‘ya’yan jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP, Leadership ta ruwaito.

Taron wanda ya gudana a makarantar IMG, Eleta, ya kuma nuna ficewar manyan masu ruwa da tsaki na APC kamar su Alhaji Abass Najeemdeen Gbayawu, Alhaji Bolaji Akinyemi Kosigiri, Engr Kayode Arowolo, da Barista Rotimi Okeowo da dai sauransu.

Da yake magana a madadin shugabannin da suka sauya shekar, Prince Olumuyiwa Akinbiyi ya bayyana cewa ba su gamsu da yadda APC ta gudanar da zabukan fidda gwani na APC da wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel