Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

  • A kalla sama da rayuka 17 sun salwanta bayan wadanda suka samu matsanantan raunuka yayin da wasu 'yan bindiga suka yi dirar mikiya wurin hakar ma'adanai a jihar Neja
  • An ruwaito yadda miyagun suka budewa mutane da jami'an tsaron wurin wuta tare da amfani da muggan makamai gami da garkuwa da mutane masu dumbun yawa
  • Sai dai, an yi nasarar garzayawa da wandanda suka samu raunuka asibiti sanadiyyar mummunan harin amma da dama daga cikinsu na mawuyacin hali

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Niger - A kalla rayuka 17 sun salwanta bayan wadanda suka samu matsanantan raunuka yayin da 'yan ta'adda suka kai farmaki mahakar ma'adanan da 'yan kasar Sin ke kula dashi tsakanin Ajata da Aboki cikin gundumar Gurmana na karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

An ruwaito yadda harin ya auku ranar Laraba da tsakar rana inda aka halaka mutane 17 duk da 'yan sandan da ke tsere mahaka ma'adanan da ma'aikata.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

'Yan bindiga
Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An gano yadda maharan suka yi dirar mikiya da miyagun makamai misalin karfe 2:00 na rana a anguwar, inda suka doshi wajan da ake hakin tare da budewa duk wanda suka yi tozali dashi wuta.

Kwamishinan tsaro da walwalar cikin gida, Emmanuel Umar, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fita ranar Alhamis, amma ya ce ba a riga an tabbatar da yawan wadanda lamarin ya ritsa dasu ba.

A cewarsa, "Gwamnatin jihar Neja na son tabbatar da yadda a rana 29 ga watan Yuni 2022 misalin karfe 2:00 rana suka samu kiran gaggawa kan yadda 'yan bindiga suka yi dirar mikiya a mahakar ma'adanan da ke tsakanin kauyen Ajata da Aboki ta gundumar Erena na karamar hukumar Shiroro, inda aka shirya tawagar tsaro zuwa wajen."
Ya kara da cewa, "An ruwaito yadda aka yi garkuwa da wasu ma'aikatan da ba a gano yawansu ba da ke wajen mahakar ma'adanan duk da 'yan kasar Sin.

Kara karanta wannan

Borno: Bidiyo ya nuna lokacin da 'yan Boko Haram 314 ke mika wuya ga jami'an sojoji

"An tura jami'an tsaro don kai samame ga 'yan ta'addan gami da ceto wadanda suka samu raunuka duk da jami'an tsaron da ke gadin wurin gami garzayawa dasu asibitin gwamnatin jihar don neman lafiyarsu.
"Yayin da gwamnatin jihar ke mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da shugabannin tsaron jihar, gwamnatin jihar ta bada tabbacin cewa sadaukarwan su ba zai tafi a banza ba."
Har ila yau, wani mazaunin yankin ya bayyanawa Daily Trust yayin wata tattaunawa yadda "kimanin mutane 11 duk da 'yan sanda bakwai da ke gadin mahakar ma'adanan da wasu mutane shida suka rasa rayukansu yayin kai harin."

Ya ce an garzaya da mutane da dama da suka samu matsanantan raunuka kuma suke cikin mawuyacin hali asibitoci don neman lafiyarsu.

Sani Yusuf Kokki, daya daga cikin wadanda suka zanta da manema labarai da wasu matasan Shiroro, sun bayyanawa Daily Trust yadda aka yi garkuwa da 'yan China da dama, inda suka siffanta lamarin a matsayin abun alhini da takaici.

Kara karanta wannan

Sokoto: 'Yan bindiga sun sace shanu yayin da suka kai hari wurin kiwonsu kusa da filin jirgi

Asali: Legit.ng

Online view pixel