Ma’aikata sun batar da fasfon Bayin Allah, maniyyata ba za su yi aikin Hajjin bana ba

Ma’aikata sun batar da fasfon Bayin Allah, maniyyata ba za su yi aikin Hajjin bana ba

  • An samu matsala da hukumar da ta ke kula da harkar alhazai ta kasar Ghana a wannan shekarar
  • Wasu maniyyatan da adadinsu ya kai 176, ba za su samu damar su sauke farali a shekarar bana ba
  • Jami’an hukumar ta Alhazai ta shaidawa maniyattan ba a san inda takardun fasfonsu suka shiga ba

Ghana - A kasar Ghana, an jefa masu niyyar yin aikin hajjin wannan shekara a tsaka mai wuya, domin an nemi takardunsu, duk an rasa.

Wani labari mara dadi da ya fito daga VOA Hausa, ya bayyana cewa akalla maniyyata 176 ne aka rasa inda takardun fasfonsu suka shiga.

Ana zargin cewa hukumar kula da alhazai na kasar Ghana, sun yi sakaci da takardun barin kasar wasu da suka biya kudin yin aikin hajji.

A dalilin wannan danyen aiki da jami’an hukumar aikin hajjin suka yi, wadannan Bayin Allah ba za su samu damar sauke farali a bana ba.

Kara karanta wannan

An Tiso Keyar Maniyattan Kano 7 Daga Saudiyya Zuwa Najeriya Saboda Biza Ta Bogi

Masu niyyar Hajji sun koka

Kamar yadda mu ka samu labari daga rahoton da aka fitar a ranar Litinin 4 ga watan Yuli, 2022, wadannan maniyyata sun nuna damuwarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka hana tafiya kasa mai tsarki, wasu sun fara yin kira ga hukumar kasar Ghana ta dawo masu da kudin da suka biya.

Aikin Hajji
Masu shirin yin Hajji Hoto: www.thenationalnews.com
Asali: UGC

Abin ya shafi mutane 176

Wadannan maniyyata sun ce jami’an kula da aikin hajji sun jibge su a filin tashi da saukar jiragen saman na garin Accra, an yi watsi da su.

Wani mutumi ya tabbatarwa manema labarai wadanda wannan matsala ta shafa sun kai 176. Har zuwa yanzu ba a ji ta bakin jami'an hukumar ba.

A cewar wannan Bawan Allah, hukumar ta fada masu cewa ba a san inda takardun fasfon suke ba, bayan sun kammala shirin sauke farali.

Kara karanta wannan

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

Idan har babu takardar nan ta fasfo, ba zai yiwu mutum ya bar kasarsa, ya iya shiga Saudi Arabiya ba, ga shi lokacin soma aikin hajjin ya karaso.

NECO ya hade da Idi

Dazu aka ji labari jarrabawar SSCE da hukumar NECO ta sa a ranar Asabar zai ci karo da bikin sallah, watakila dole sai an canza ranar kenan.

Shugaban kungiyar MURIC mai zaman kanta, Farfesa Ishaq Akintola ya ja hankalin hukumar, ko da ya yi wa NECO uzurin kicibis din da aka samu.

Alhazan Neja sun makale

A ranar Litinin, Legit.ng Hausa ta tuntubi wani daga cikin masu niyyar zuwa aikin Hajjin wannan shekara daga jihar Neja domin jin irin halin da suke ciki.

Kamar yadda wannan Alhaji ya shaida mana a jiya, an dauko su daga Minna zuwa garin Abuja domin a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe za a dauke su.

Kara karanta wannan

Tawagar shugaban kasa basu tabuka komai ba a lokacin da yan bindiga suka auka masu – Mazauna kauyukan Katsina

Mun fahimci cewa har yanzu ba a kira sahun karshe na Maniyyatan jihar zuwa Abuja ba. Akalla jirage biyu ake sa ran an yi jigilarsu zuwa kasa mai tsaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel