2023: 'Yan Najeriya sun kagu a fatattaki APC a kasa, inji dan takarar NNPP Kwankwaso

2023: 'Yan Najeriya sun kagu a fatattaki APC a kasa, inji dan takarar NNPP Kwankwaso

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya kai ziyarar bude ofishin jiha a Gombe, ya yi maganganu masu daukar hankali
  • Kwankwaso, wanda ya samu tarba daga Gombawa ya bayyana jin dadinsa tare da fadin shirye-shiryensa na 2023
  • Ya kuma ce, alamu masu karfi sun nuna cewa, 'yan Najeriya sun kagu da ganin karshen mulkin Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Gombe - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Alhaji Rabi’u Kwankwaso, ya ce daga dukkan alamu ‘yan Najeriya sun gaji da jam’iyyar APC mai mulki, kuma suna da burin ganin karshen gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kwankwaso ya yabawa dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa a jihar Gombe da yammacin ranar Asabar, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama da ke nuna cewa jama’a a shirye suke don samun damar kawar da gwamnatin APC a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba zai yiwu na yiwa Peter Obi mataimaki ba, Kwankwaso

Kwankwaso ya hango karshen APC a zaben 2023
2023: 'Yan Najeriya sun kagu a fatattaki APC a kasa, inji dan takarar NNPP Kwankwaso | Hoto: arise.tv
Asali: UGC

Kwankwaso, wanda ya je Gombe domin kaddamar da ofishin jam’iyyar, ya ce dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa daga filin jirgin sama zuwa cikin garin, sun zaburar da shi cewa jihar Gombe ta shiga sahun su Kano wajen jihohin Kwankwasiyya.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a otal din Gombe na kasa da kasa, jim kadan bayan kaddamar da ofishin, Kwankwaso ya ce akwai manyan alamu na kyakkyawar makoma ga jam’iyyar da ba ta kai watanni hudu ba da yin kaurin suna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, NNPP za ta kawo wa ‘yan Najeriya sauyi mai kyau ta hanyar share hawaye da wahalhalun da gwamnatin Buhari ta sanya su, inji rahoton gidan talabijin na Arise.

A cewarsa:

“Jami’an gwamnatin APC masu hadama sun durkusar da duk wani bangare na tattalin arzikin Najeriya, in ban da aljihunsu.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shawarci Obi da ya zama abokin takararsa, ya bayyana muhimman dalilai

Ya kuma bukaci jama’a da su fito su karbi katin zabensu na dindindin (PVCs), domin hakan ne kawai zai kai ga kawo sauyi a kasar.

NNPP za ta kawo wuta a zaben 2023, Buba Galadima

A nasa jawabin, shugaban kwamitin amintattu na NNPP, Buba Galadima, ya ce zaben 2023 zai yi wa jam’iyyar NNPP murmushi, ganin yadda aka karbe su a jihar Gombe, rahoton Tribune Online.

Galadima ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su je su nemi katinan su na PVC tare da jan hankalin ‘yan Nijeriya a duk sassan jihar, musamman a kauyuka da su ma su yi hakan.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Alhaji Ahmed Mailantarki, ya godewa dan takarar shugaban kasa bisa ziyarar da ya kai masa, ya kuma ba shi tabbacin cewa ofishin jam’iyyar zai kara inganta ayyukan yakin neman zabensu a Gombe.

Mailantarki ya ce jam’iyyar NNPP a jihar Gombe ta dogara sosai ga ikon talakawa, wadanda su ne kashin bayan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Ya ce NNPP ta samu goyon bayan al’ummar Gombe ne saboda sun bi sahun Kwankwaso, wanda ya baiwa matasa damar cikar burinsu da kuma damar da suke da ita a bangarori daban-daban.

A kalamansa:

“Ta hanyar kwaikwayar abubuwan da ka gada, mun sami damar tura wasu matasa ‘yan Najeriya takwas zuwa Turai da sauran sassan duniya domin cika burinsu na kwallon kafa, kuma har yanzu muna shirin kara habaka irin wannan shiri.”

Kwankwaso: Abin da ya sa Peter Obi ba zai iya lashe zaben shugaban kasa a Jam’iyyar LP ba

Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP, ya ce Labour Party ba za ta iya lashe zabe ba.

A wata hira da aka yi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a shirin siyasar nan na Politics Today a gidan talabijin na Channels, ya yi magana a kan shirin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

Legit.ng Hausa ta bibiyi wannan hira, inda aka ji Kwankwaso yana magana a game da Peter Obi, duk da bai fito ya ambaci sunan ‘dan takaran LP karara a hirar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel