Hotuna: Matawalle ya kaddamar da rundunar CPG don yaki da 'yan bindigan Zamfara

Hotuna: Matawalle ya kaddamar da rundunar CPG don yaki da 'yan bindigan Zamfara

  • Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kaddamar da sabuwar rundunar tsaro ta gadin al'umma a jiharsa
  • Ya kaddamar da wannan rundunar tsaron al'ummar ne a ranar Asabar, lokacin da ta'addanci yayi kamari a jihar
  • Kamar yadda gwamnan ya bayyana, rundunar tsaron tana da alhakin bai wa yankunan jihar kariya tare da magance matsalar 'yan bindiga

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kaddamar da sabuwar rundunar dakarun gadin al'umma wacce za ta magance ta'addanci na 'yan bindiga a jiharsa.

Kamar yadda hotunan suka nuna, dakarun suna da kayan aiki masu launin ja da baki wanda ke bayyana 'ko a mutu, ko a yi rai'.

Gwamnan ya kaddamar da wannan rundunar tsaron ne a ranar Asabar, lokacin da ta'addancin 'yan bindiga yayi kamari a fadin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

Ga hotunan a kasa:

Dakarun CPG
Hotuna: Matawalle ya kaddamar da dakaru masu gadin al'umma a Zamfara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dakarun CPG
Hotuna: Matawalle ya kaddamar da dakaru masu gadin al'umma a Zamfara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Dakarun CPG
Hotuna: Matawalle ya kaddamar da dakaru masu gadin al'umma a Zamfara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Dakarun CPG
Hotuna: Matawalle ya kaddamar da dakaru masu gadin al'umma a Zamfara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bawa kai kariya: Gwamna Matawalle ya kaddamar da kwamitoci, ya rarraba motoci da babura

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kaddamar da kwamitin tsaro guda 4 gami da samar da motoci 20 kirar Hilux da babura 1,500 don fara daukar matakai. Sakataran watsa labaran gwamnan, Jamilu Iliyasu Magaji ne ya bayyana hakan ranar Talata.

Kwamitin sune kwamiti na musamman don tattara bayanan sirrin ta'addanci, kwamitin kula da tsaron anguwa (CPG), kwamitin gurfanar da masu laifukan da suka shafi ta'addanci, da kwamitin tabbatar da tsaron jihar.

Matawalle ya ce kafa kwamitin wani bangare ne na kokarin da mulkinsa ke yi ba tare da gajiyawa don shawo kan annobar matsalar rashin tsaro da ta dauki tsawon lokaci tana addabar jihar da sauran jihohin yankin arewa-maso- yamma.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna El-Rufai, Ganduje da wasu jagororin arewa zasu sa labule da Tinubu kan zaɓo mataimakinsa na gaske

Asali: Legit.ng

Online view pixel