Gwamna El-Rufai, Ganduje da wasu shugabannin arewa zasu gana da Tinubu kan mataimakinsa a 2023

Gwamna El-Rufai, Ganduje da wasu shugabannin arewa zasu gana da Tinubu kan mataimakinsa a 2023

  • Yankin arewa ta yamma ya naɗa wasu wakilai da zasu nemi zama da Tinubu don tattauna wasu muhimman batutuwa game da 2023
  • Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai, da gwamna Ganduje na cikin wakilan da taron shugabannin yankin ya naɗa a Kaduna
  • Taron ya samu halartar gwamnoni, yan takarar gwamna, Ministoci da sauran shugabanni yan yankin arewa ta yamma

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jagororin APC na arewa-yamma sun naɗa tawagar wakilai da zasu je su gana da ɗan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, kan wasu "abun kula" game da zakulo wanda zai zame masa mataimaki.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai da gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na cikin waɗan da aka naɗa su ga Tinubu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna El-Rufai, Ganduje da wasu shugabannin arewa zasu gana da Tinubu kan mataimakinsa a 2023 Hoto: Punchng
Asali: Facebook

An cimma wannan matsayar ne a wurin taron jagororin shiyyar arewa ta yamma, da suka haɗa da gwamnoni, yan takarar gwamna, Ministoci da sauran su, wanda ya gudana a Kaduna

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya magaantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a PDP, ya faɗi matakan da suke ɗauka

A wata sanarwa da mataimakin shugaban APC na arewa ta yamma, Salihu Lukman ya fitar ranar Alhamis, ya ce taron ya yi na'am da fara tarukan neman shawarwari don kara karafafa APC a yankin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, gwamnoni da masu rike da Ofisoshin siyasa sun kara nazari da duba halin da jam'iyya ta tsinci kanta a matakin ƙasa da na shiyyoyi.

Haka nan kuma sun gano tare da tattara kalubalen da APC ke kwana da tashi da su a wasu jihohi, kana suka cimma matsayar ƙara nunka kokarin da ake na rarrashi da sulhunta juna.

A sanarwan, Lukman ya ce:

"Taron ya taɓo gudummuwar da arewa maso yamma ta bayar wajen kafawa da yaɗuwar APC da kuma nasararta a zaɓe, tare da sanin cewa yankin ne ya samar da kaso 39% na kuri'un da APC ta samu a zaɓen shugaban kasa na 2019 da 2015."

Kara karanta wannan

Katsina: Masari ya sake nada kwamishinoninsa bayan sun sha kaye a zaben fidda gwani

"Saboda haka shiyyar arewa ta yamma ta amince ta tattara bukatunta da muhimman abun damuwa kuma daga bisani zata zauna da Tinubu ta ɓaje masa komai ɗaya bayan ɗaya."

Vanguard ta rahoto cewa jagororin APC na arewa maso yamma sun ɗauki matakin ne yayin da yawon neman shawarin masu ruwa da tsaki kan wanda ya dace ya zaɓa a matsayin abokin takara.

Ɗan takarar APC ya miƙa sunan Kabir Masari daga Katsina, arewa maso yamma, a matsayin abokin takararsa ga hukumar INEC. Wata majiya tace an saka sunan Masari ne a matsayin riko.

A wani labarin kuma Gwamnan arewa ya canza mataimaki, ya zaɓi mace shugabar jami'a a zaɓen 2023

Gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar PDP ya zaɓi shugabar jami'ar ADSU a matsayin wacce zata zama abokiyar takararsa a 2023.

Ahmadu Umaru Fintiri ya ɗauki wannan matakin ne bayan jam'iyyar APC ta tsayar da mace takarar gwamnan jihar a 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC ya faɗi babban laifin INEC da ya jawo batan takardun Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel