Hotunan Dawowar Buhari Gida Abuja Bayan Kai Ziyara Portugal

Hotunan Dawowar Buhari Gida Abuja Bayan Kai Ziyara Portugal

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baro Lisbon, Portugal kuma ya dawo gida Abuja a ranar 2 ga watan Yulin shekarar 2022.

Buhari Sallau, hadimin Shugaba Buhari a bangaren watsa labarai ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.

Shugaba Buhari, tare da jakadan Najeriya a Portugal, Ambasada Alex Kefas sun dauki hoto da jami'an ofishin jakadancin Najeriya a Portugal jim kadan kafin ya baro Lisbon, don dawowa Abuja.

Buhari tare da ma'aikatan ofishin jakadancin Najeriya a Portugal.
Hotunan Dawowar Buhari Gida Abuja Bayan Kai Ziyara Portugal. Hoto: Buhari Sallau.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari yana shiga jirgi don dawowa Abuja.
Hotunan Dawowar Buhari Gida Abuja Bayan Kai Ziyara Portugal. Hoto: Buhari Sallau.
Asali: Facebook

Buhari ya dawo daga Lisbon.

Hotunan Obasanjo Ya Kwaso Fasinjoji A Adaidaita Sahu Ya Kayyatar Da Al'umma

A wani rahoton, tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a murnar cikarsa shekaru 85 ya tuka babur din adaidaita sahu a titunan Abeokuta.

Kara karanta wannan

Hotunan Obasanjo Ya Kwaso Fasinjoji A Adaidaita Sahu Ya Kayyatar Da Al'umma

Tsohon shugaban kasar ya cika shekaru 85, a ranar 5 ga watan Maris, an hange shi yana daukan fasinjoji a cewar wasu hotuna da aka gani a shafin Daniel Sync Olusanya, wani mai daukan hotu dan Najeriya mazaunin Landan daga Ijebu, Jihar Ogun.

A cewar wani rahoto da The Cable ta wallafa, Obasanjo, a watan Yuni, ya raba wa mutum 85 baburan adaidaita sahu a yayin murnar cikarsa shekaru 85.

Asali: Legit.ng

Online view pixel