'Yan bindiga sun ɗana Bom a Ofishin yan sanda, sun halaka babban Jami'i a Kogi

'Yan bindiga sun ɗana Bom a Ofishin yan sanda, sun halaka babban Jami'i a Kogi

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari Caji Ofis da ke yankin Eika-Ohizenyi a ƙaramar hukumar Okeji, jihar Kogi da tsakar dare
  • Maharan sun kashe Insufektan yan sanda yayin musayar wuta, sun tashi Bam da ya lalata wani sashin ginin Ofishin
  • Tuni dai hukumar yan sanda ta tura karin dakaru yankin domin ƙara tsaurara tsaro da nufin cafke maharan

Kogi - 'Yan bindiga sun farmaki Ofishin yan sanda na yankin Eika-Ohizenyi, ƙaramar hukumar Okehi, jihar Kogi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Bayanai sun nuna cewa 'yan bindiga sun kai harin ne ɗauke da abubuwan fashewa da sanyin safiyar Jumu'a 24 ga watan Yuni, 2022.

Yayin harin, Jami'in ɗan sanda mai muƙamin Insufekta ya rasa rayuwarsa yayin da wani sashin Caji Ofis ɗin ya yi kaca-kaca.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a mazaɓar Ahmad Lawan ya bude sabon shafi, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

Ofishin yan sandan a yankin jihar Kogi da aka kai hari.
'Yan bindiga sun ɗana Bom a Ofishin yan sanda, sun halaka babban Jami'i a Kogi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwiato Wani mazaunin yankin, Mallam Momoh Abubakar, ya ce maharan sun mamaye caji Ofis ɗin da ƙarfe 12:15 na dare ɗauke da Bama-bamai da wasu makamai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce Bom ɗin da suka fara jefa wa Ofishin ya yi ƙara mai karfi wacce ta tashi da yawan mazauna yankin daga bacci, a cewarsa Bam ɗin ya ruguza sassan caji Ofis ɗin.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kogi, William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Aya ya bayyana cewa Kwamishinan yan sandan jihar, Edward Egbuka, ya ziyarci wurin kuma tuni aka ƙara jibge jam'ian tsaro a yankin.

A sanarwan, kakakin yan sandan ya ce:

"Wani sashin Ofishin ya ƙone sakamakon abun fashewa da maharan suka yi amfani da shi. Abin takaicin shi ne Insufekta ya rasa rayuwarsa yayin musayar wuta kafin sojoji su kawo ɗauki wanda ya tilasta wa maharan suka tsere."

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Ɗan majalisa ya tausaya wa Malaman Jami'a, ya basu tallafin makudan kuɗi

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya ba da umarnin ƙara girke jami'an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da kwantarwa mutane hankali.

A wani labarin kuma Abinda Sanata Ekweremadu da matarsa suka faɗa wa Kotu a Landan kan tuhumar da ake musu

Sanata Ike Ekweremadu da matarsa sun gurfana a gaban Kotun Majirstire a Landan, kuma sun yi kokarin kare kan su kan zargin safara.

Ta bakin lauyoyin su, Gavin Irwin da Antonia Gray, sun musanta tuhumar da ake musu na safarar mutane da nufin yanke sassan jikin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel