Da Ɗumi-Ɗumi: Sabon rikici ya kunno kai a Yobe ta arewa, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

Da Ɗumi-Ɗumi: Sabon rikici ya kunno kai a Yobe ta arewa, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

  • Sabon rikici ya sake kunno kai game da zaɓen fidda gwanin jam'iyyar APC na ɗan takarar Sanatan Yobe ta arewa
  • Yayin da aka ja daga tsakanin Machina da Ahmad Lawan, wani ɗan takara daban ya ƙalubalanci nasarar Machina a Kotu
  • Ya ce a tafka maguɗi a zaben kasancewar ba'a saka sunansa cikin jerin yan takara ba duk da ya halarci wurin

Yobe - Rikici kan tikitin takarar Sanata mai wakiltar Yobe ta arewa ya buɗe sabon babi, yayin da wani ɗan takara, Abubakar Abubakar Jinjiri, ya ƙalubalanci nasarar Bashir Sheriff Machina, a Kotu.

Machina, wanda ya samu kuri'u 289 da zaɓen fidda gwani, yanzu haka yana fafatawa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan kan tikitin.

Sanata Lawan ya sha kasa a zaben fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, amma Machina ya ƙi ya janye masa tikitin Sanatan Yobe ta arewa.

Kara karanta wannan

Dambarwa ta sake ɓallewa a siyasar Kano, Ɗan majalisa ya nemi Kotu ta soke ɗan takarar gwamna na APC

Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan.
Da Ɗumi-Ɗumi: Sabon rikici ya kunno kai a Yobe ta arewa, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu Hoto: Ahmad Lawan
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa jam'iyyar APC ta miƙa sunan Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar da ta tsayar a mazaɓar Yobe ta arewa, lamarin da ya tilasta wa Machina neman haƙƙinsa a Kotu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa ya kai ƙarar Machina gaban Kotu?

Jinjiri na ɗaya daga cikin ɓangarorin da aka lissafo a ƙarar gaban Mai Shari'a Fadima Murtala Aminu ta babbar Kotun tarayya da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ranar Jumu'a.

Lauyan ɗan takaran, Barista Usman Lukman Nuhu, ya shaida wa jaridar cewa wanda yake wa aiki na ƙalubalantar Machina, APC ta jiha da ta ƙasa da hukumar zaɓe INEC, kan zare sunansa a zaɓen fidda gwani.

Ya ce ƙiri-kiri aka zare sunan Jinjiri aka hana shi fafatawa a zaɓen fidda ɗan takarar Sanatan duk da ya hallara wurin.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Ɗan majalisa ya tausaya wa Malaman Jami'a, ya basu tallafin makudan kuɗi

Lauyan ya ce:

"Ina da yaƙinin kun ga takardar Sakamakon zaɓen fidda gwanin, idan kuka diba babu sunan wanda nake karewa kuma babu kuri'un da ya samu a takardan."

Ya ce ƙin sanya sunan ɗan takara ya saɓa wa sashi na 84 (3) da 84 (4) na sabon kundin dokokin zaɓe 2022.

Bayan haka an gabatar da sauran korafe-korafe Bakwai da suka biyo bayan zaɓen fidda gwanin APC. Kotu ta ɗage sauraron dukkan su zuwa ranar 21 ga watan Yuli, 2022.

A wani labarin kuma Rikici ya dawo ɗanye, ɗan majalisa ya buƙaci Kotu ta soke ɗan takarar gwamnan Kano na APC

Mamba a maja lisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar birnin Kano, Sha'aban Sharaɗa, ya nemi Kotu ta soke takarar Gawuna na APC.

Ɗan majalisar ya ce Ɗan takarar da jam'iyyar APC sun saba wa sabon kundin dokokin zaɓe 2022 a wurin zaɓen fidda gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel