Yajin aikin ASUU: Ɗan majalisa ya tausaya wa Malaman Jami'a, ya basu kuɗaɗe

Yajin aikin ASUU: Ɗan majalisa ya tausaya wa Malaman Jami'a, ya basu kuɗaɗe

  • Yayin da yajin aikin ASUU ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, wani ɗan majalisa a jihar Kuros Riba ya tausaya wa halin da Lakcarori ke ciki
  • Mamba a majalisar dokokin jihar, Mista Hilary Bisong, ya tallafawa Lakcarori yan asalin mazaɓarsa da kudi N900,000
  • Malaman Jami'ar ta jihar Kalaba da suka amfana da tallafin, sun yaba wa ɗan majalisan tare da masa fatan Alheri

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Cross River - Wani ɗan majalisar dokoki a jihar Kuros Riba, Hilary Bisong, ya tallafawa malaman Jami'ar Kalaba da kuɗi N900,000 don rage radaɗi yayin da yajin aikin ASUU ya ƙi karewa.

Mista Bisong, mamba ne mai wakiltar mazaɓar jiha Boki 2 a majalisar dokokin jihar Kuros Riba, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa Malaman Jami'ar da suka amfana da tallafin sun fito ne daga mazaɓar Honorabul Bisong.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a mazaɓar Ahmad Lawan ya bude sabon shafi, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

Hilary Bisong.
Yajin aikin ASUU: Ɗan majalisa ya tausaya wa Malaman Jami'a, ya basu kuɗaɗe Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake damƙa musu tsabar kuɗin ranar Jumu'a a Kalaba, Bisong, ya ce ya basu tallafin ne da nufin rage radaɗin dakatar musu da Albashi na tsawon watanni huɗu saboda yajin aikin ƙungiyar ASUU.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar ɗan majalisar, Lakcarorin waɗan da mambobi ne na ƙungiyar ASUU, sun cancanci a tallafa musu da kuma basu kulawa a irin wannan lokacin.

Bisong ya ce:

"Waɗan nan Lakcarorin suna da iyalai da ke jira daga wurin su kuma suna biyan Bil, da ya haɗa da na lafiya da sauran harkokin yau da kullum. Don haka akwai buƙatar mu taimaka musu a wannan lokacin."
"Mutanen da suka amfana da tallafin, waɗan da Lakcarori ne a jami'ar UNICAL, dukkan su mutanen mazaɓata ne."
"Addu'ata ita ce tattaunawar da ake tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya ya haifar da sakamakon da mutane ke tsammani domin Malamai su samu damar komawa aji."

Kara karanta wannan

Dambarwa ta sake ɓallewa a siyasar Kano, Ɗan majalisa ya nemi Kotu ta soke ɗan takarar gwamna na APC

Abinda Malaman Jami'ar suka ce ga ɗan majalisar su

Ɗaya daga cikin lakcarorin da suka amfana da tallafin, Paul Bukie, ya yaba wa ɗan majalisar bisa, "tunawa da su a wannan lokacin na gwagwarmaya."

Mista Bukie ya ƙara da cewa tallafin da suka karɓa, zai taimaka musu matuƙa wajen rage yawan bukatun su.

Wani daban daga cikin waɗan da suka amfana, Jerry Etta, ya roki Allah ya yi wa ɗan Majalisar Albarka bisa wannan taimako da ya ba su.

A wani labarin kuma Kwanaki kaɗan bayan ficewa daga PDP, Tsohon minista ya sa labule da gwamna Wike

Kwanaki kaɗan bayan ya yi murabus daga PDP, Tsohon ministan Neja Delta, Chief Orubebe, ya gana da gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Taron mutanen biyu ya gudana ne a gidan Wike dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas kuma a sirrance, ba su ce komai ba bayan fitowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel