Tsaro: Sheikh Gumi Ya Gargadi Jami'an Tsaro Kan Kama Matasan Fulani Barkatai Da Sunan Yaki Da Yan Bindiga

Tsaro: Sheikh Gumi Ya Gargadi Jami'an Tsaro Kan Kama Matasan Fulani Barkatai Da Sunan Yaki Da Yan Bindiga

  • Shiekh Ahmad Gumi ya yi gargadi da jami'an tsaro su guji kama matasan makiyaya fulani barkatai da sunan yaki da yan bindiga a Najeriya
  • Babban malamin addinin musuluncin mazaunin Jihar Kaduna ya yi wannan gargadin ne a wurin taron kaddamar da kungiya ta kare hakkin makiyaya mai suna Nomadic Right Concern Group
  • Farfesa Umar Labdo, shugaban kungiyar na kasa ya ce kungiyar ba ta Fulani ne kadai ba, amma dukkan makiyaya, daga kowanne kabila, yanki da addini

Jihar Kaduna - Fittacen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargadi hukumomin tsaro game da kama matasan fulani barkatai da suna yaki da ta'addanci, rahoton Daily Trust.

Da ya ke magana a wurin taron kaddamar da Kungiyar Kare Hakkin Makiyaya a Kaduna, Sheikh din ya ce kawo yanzu, akwai matasan fulani da yara da yawa a wadanda ba su ji ba ba su gani ba a tsare.

Kara karanta wannan

Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu

Shiekh Ahmad Gumi.
Sheikh Gumi: A Dena Kama Matasan Fulani Ba Bisa Ka'ida Ba Da Sunan Yaki Da Yan Bindiga. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dalilin kafa kungiyar shine tabbatar da cewa matasan Fulani da ba su aikata komai ba sun samu adalci, ya kara da cewa za ta taimaka wurin kawo zaman lafiya a kasar.

"Kwanaki kadan da suka gabata, wani mutum ya kira ni ya ce jami'an tsaro sun kama yara bakwai da ba su aikata laifi ba a ranar 17 ga watan Mayun 2022 kuma tun ranar babu labarinsu. Akwai kuma labaran batar matasan Fulani da yara ba tare an sake ganinsu ba.
"Akwai wadanda ake tsare wa ko a tura gidan yari na shekaru babu shari'a. Idan wani ya aikata laifi, doka ya ce a kai shi kotu cikin awa 24 amma ana ajiye matasan nan tsawon shekaru babu shari'a, wasu sun mutu a tsare. Bai kamata wannan na faruwa a kasar nan ba.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Sake Jaddada Cewa Sai An Ladabtar Da 'Yan Ta'adda, Ya kwatantasu da Ragwaye

"An kafa kungiyar Nomadic Right Concern Group ne don nema wa yaran da aka kama ba tare da laifi ba adalci. Wadanda aka samu da laifi a hukunta su yadda doka ya tanada amma wadanda ba su da laifi a sake su saboda adalci da daidaito. Dole a dena kama matasa da yara barkatai," in ji shi.

Ya yi bayanin cewa cikin ayyukan kungiyar, akwai gano adadin yaran Fulani wadanda aka tsare da su kuma ba su da laifi da neman lauyoyi da za su fitar da su.

Jawabin shugaban Kungiyar Farfesa Umar Labdo

Da ya ke magana kan kafa kungiyar, Shugabanta Farfesa Umar Labdo, ya ce kungiyar ba ta Fulani ne kadai ba, amma dukkan makiyaya, daga kowanne kabila, yanki da addini.

Ya ce kungiyar za ta zama murya ga makiyaya da ba su da karfin fada a ji inda za su iya yi wa kasa bayanin matsalolinsu da bukatunsu da abin da suke fatan cimma.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa da Mutane Sun ci mu Tarar N1m Saboda Lattin Kai Kudin Fansa, Mata da Miji

Sheikh Gumi: A wurin tsagerin Niger Delta ƴan bindiga suka koya satar mutane

A wani rahoton, Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi yana cigaba da kira ga gwamnati ta yi wa yan bindiga da ke kai hare-hare a arewacin Nigeria afuwa, News Wire NGR ta ruwaito.

Gumi, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na AIT a ranar Talata 16 ga watan Fabarairu ya ce a wurin tsagerun Niger Delta yan bindigan suka koya yin garkuwa da mutane don haka a musu afuwa kamar yadda aka yi wa yan Niger Deltan.

A cewar malamin, bata garin da ke cikin makiyaya tsiraru ne kuma sauran sun dauki makamai ne domin kare kansu bayan an sace musu shanunsu wanda shine ke matsayin 'man fetur' din su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel