Sheikh Gumi: A wurin tsagerin Niger Delta ƴan bindiga suka koya satar mutane

Sheikh Gumi: A wurin tsagerin Niger Delta ƴan bindiga suka koya satar mutane

- Malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya cigaba da kira da gwamnati ta yi wa makiyaya afuwa

- Malamin ya ce daga wurin tsagerun Niger Delta bata garin makiyaya suka koyi garkuwa da mutane

- Gumi ya ce tsiraru ne bata gari cikin makiyaya kuma saura sun dauki makami ne don kare kansu

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi yana cigaba da kira ga gwamnati ta yi wa yan bindiga da ke kai hare-hare a arewacin Nigeria afuwa, News Wire NGR ta ruwaito.

Gumi, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na AIT a ranar Talata 16 ga watan Fabarairu ya ce a wurin tsagerun Niger Delta yan bindigan suka koya yin garkuwa da mutane don haka a musu afuwa kamar yadda aka yi wa yan Niger Deltan.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaban kamfen ɗin Atiku, Gbenga Daniel, ya fice daga PDP ya koma APC

Sheikh Gumi: A wurin tsagerin Niger Delta ƴan bindiga suka koya satar mutane
Sheikh Gumi: A wurin tsagerin Niger Delta ƴan bindiga suka koya satar mutane. Hoto: @lindaikeji
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu sarakunan yankin Yarbawa na aiki tare da makiyaya da ke garkuwa, Sanata Fadahunsi

A cewar malamin, bata garin da ke cikin makiyaya tsiraru ne kuma sauran sun dauki makamai ne domin kare kansu bayan an sace musu shanunsu wanda shine ke matsayin 'man fetur' din su.

Gumi ya ce;

"Ba mu sauya sabon tsari bane kan yadda muke kokarin warware matsalar shiyasa har yanzu muke a nan. Kuma da muke ce afuwa, ba mu nufin duk wanda aka samu da laifin kisa ya tafi haka nan.
"A wurin yan kungiyar MEND suka koyi garkuwa. Ban ga wani banbanci ba. Sune aka fara sace wa dabobinsu. Shanunsu ne man fetur dinsu. Ina iya cewa kashi 10 cikin 100 na makiyaya ne bata gari ba kashi 90 ba, daga karshe sun dauki makamai ne don kada a karar da su.
"Su da kansu za su iya maganin sauran bata garin da ke cikinsu saboda ba su son wani ya janyo musu fitina."

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel