Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace DPO na yan sanda, Mutane sun shiga tashin hankalo

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace DPO na yan sanda, Mutane sun shiga tashin hankalo

  • Wasu miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da DPO na yankin ƙaramar hukumar Eggon a jihar Nasarawa yana aikin dare
  • Rahoto ya nuna cewa duk wani kokarin ji daga DPO Haruna Abdulmalik ya ci tura tun bayan faruwar lamarin a kan hanyar Bakano ta yankin
  • Tuni dai masu garkuwan suka nemi iyalin babban ɗan sandan, inda suka buƙaci a tattara musu kuɗi miliyan N5m a matsayin fansa

Nasarawa - 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban jami'an yan sanda (DPO) mai kula Caji Ofis din ƙaramar hukumar Eggon a jihar Nasarawa, CSP Haruna Abdulmalik.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa maharan sun tafi da DPO zuwa wani wuri da ba'a sani ba da daren ranar Laraba, 22 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sako Sarkin da suka nemi Miliyan N150m fansa a jihar Arewa

Rahoto ya nuna cewa jami'in ɗan sandan na kan aikinsa na Sintiri a kan hanyar Nasarawa Eggon – Akwanga da daddare lokacin da ya ci karo da yan bindigan a kusa da Bakano.

DPO a jihar Nasarawa.
Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace DPO na yan sanda, Mutane sun shiga tashin hankali Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A ƴan bayanan da manema labarai suka tattara a yanzu da muke kawo muku wannan rahoto ya nuna cewa yan ta'addan sun tasa DPOn zuwa maɓoyarsu da ba'a sani ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma wani rahoto ya bayyana cewa har maharan sun nemi iyalan ɗan sandan, sun buƙaci a tattara musu miliyan N5m a matsayin kuɗin fansa.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Eggon, Injiniya Benjamin Kuze, ya tabbatar da rahoton garkuwa da CSP Haruna.

Ya ce yan bindigan sun yi garkuwa da babban jami'in yan sandan ƙaramar hukumar da misalin ƙarfe 9:00 na dare a kan hanyar Bakano.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

Ya ƙara da cewa, "Duk wani kokarin da aka yi na tuntuɓar DPO ta wayar salula ya ci tura tun bayan faruwar lamarin."

Duk wani yunkuri na tabbatar da faruwar lamarin daga hukumar yan sanda reshen jihar Nasarawa bai samu nasara ba zuwa yanzu.

A wani labarin kuma Dakarun Amotekun sun kama wasu daga cikin maharan da suka aikata mumminan ta'addanci kan masu ibada a garin Owo

Duk da ba'a bayyana adadin mutanen da suka shiga hannu ba amma kwamandan Amotekun ya ce ba zasu huta ba sai sun kama maharan baki ɗaya.

A ranar 5 ga watan Yuni, wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba suka kai hari Cocin Katolika a Owo, inda suka kashe kusan masu ibada 40.

Asali: Legit.ng

Online view pixel