Da Dumi-Ɗumi: Babban Sarki Mai Daraja da Yan Bindiga Suka Sace Ya Kuɓuta

Da Dumi-Ɗumi: Babban Sarki Mai Daraja da Yan Bindiga Suka Sace Ya Kuɓuta

  • Yan bindiga sun sako Babban Basarake, Hakimin Masarautar Panyam, karamar hukumar Mangu a jihar Filato
  • Bayan garkuwa da Sarkin mai daraja, yan bindiga sun nemi miliyan N150m a matsayin kuɗun fansa, suka dawo miliyan N10m
  • Dandazon mutane har da wasu sarakuna ne suka tarbi Sarkin yayin dawowarsa cikin fada ranar Alhamis da safe

Plateau - Basaraken Panyam dake ƙaramar hukumar Mangu jihar Filato, Mai Martaba Aminu Derwan, wanda aka sace har cikin fadarsa ya shaƙi iskar yanci.

Wata majiya daga masarautar ta shaida wa The Nation cewa maharan sun sako Sarkin ne da misalin karfe 11:45 na daren ranar Laraba don ya koma cikin iyalansa.

Taswirar jihar Filato.
Da Dumi-Ɗumi: Babban Sarki Mai Daraja da Yan Bindiga Suka Sace Ya Kuɓuta Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Majiyar ta ƙara da cewa Derwan ya iso fadarsa dake Panyam ranar Alhamis da safe a tsakiyan dandazon mutanensa da wasu masu riƙe da Sarauta da ke farin cikin dawowarsa.

Kara karanta wannan

Layukan Wayan Ekweremadu Da Na Kakakinsa A Kashe, Yayin Da Aka Kama Shi Da Matarsa A Landan

Shin makusantansa sun biya kuɗin fansa?

Wasu bayanai da jaridar ta tattara sun nuna cewa masu garkuwan da suka sace shi, waɗan da tun farko suka nemi Miliyan N150 kuɗin fansa, sun sakko zuwa miliyan N10m da safiyar Laraba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk wani ƙoƙari na jin cikakken bayani kan ko iyalan Basaraken sun biya miliyan N10m kafin sako shi ya ci tura kasancewar iyalan sun ƙi cewa komai kan lamarin.

Haka nan duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin hukumar yan sandan Filato, DSP Alfred Alabon, be yi nasara ba, amma wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar da sako Sarkin.

A ranar Litinin da ta gabata, wasu yan bindiga kusan 20 suka yi awon gaba da Basaraken, Hakimin Panyam bayan sun mamaye fadarsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

Derman ne basarake na uku da aka yi garkuwa da shi a yankin ƙaramar hukumar ta Mangu a baya-bayan nan, lamarin da ya jefa tashin hankali a tsakanin mutane.

A wani labarin na daban kuma Ana kama yan ta'addan da suka kashe masu ibada 40 a Cocin Owo, jihar Ondo

Jami'an tsaro na musamman a jihar Ondo, Amotekun, sun yi nasarar kama wasu da ake zargin suna da hannun a harin Cocin Owo.

Duk da ba'a bayyana adadin mutanen da suka shiga hannu ba amma kwamandan Amotekun ya ce ba zasu huta ba sai sun kama maharan baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel