Da Ɗumi-Dumi: An kama yan ta'addan da suka kashe masu ibada 40 a Owo

Da Ɗumi-Dumi: An kama yan ta'addan da suka kashe masu ibada 40 a Owo

  • Jami'an tsaro na musamman a jihar Ondo, Amotekun, sun yi nasarar kama wasu da ake zargin suna da hannun a harin Cocin Owo
  • Duk da ba'a bayyana adadin mutanen da suka shiga hannu ba amma kwamandan Amotekun ya ce ba zasu huta ba sai sun kama maharan baki ɗaya
  • A ranar 5 ga watan Yuni, wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba suka kai hari Cocin Katolika a Owo, inda suka kashe kusan masu ibada 40

Ondo - Rundunar jami'an tsaro ta jihar Ondo Amotekun ta ce ta kama wasu mutane da take zargin suna da hannu a harin da aka kai Cocin Katolika da ke Owo, ƙaramar hukumar Owo.

The Nation ta ruwaito cewa Amotekun ta ce ta kuma gano wasu makamai da Motoci, waɗan da maharan suka yi amfani da su wajen kai harin ta'addancin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Wurin da aka kai hari a Owo.
Da Ɗumi-Dumi: Ana kama yan ta'addan da suka kashe masu ibada 40 a Owo Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kusan mutane 40 da suka je ibada ne suka rasa rayukansu, wasu 70 suka jikkata a harin wanda aka kai Cocin St Francis Catholic Church, Owo, ranar 5 ga watan Yuni, 2022.

Kwamandan dakarun Amotekun na jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ya ce sun cafke wasu da ake zargin suna da alaka da kai kazamin harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zamu cafke sauran baki ɗaya - Kwamandan Amotekun

Sai dai kwamandan bai faɗi adadin waɗan da suka kama ba, amma a rahoton jaridar Punch, ya nuna tabbacin cewa ba zasu rintsa ba har sai sun kama baki ɗaya maharan wurin Ibada a Owo.

Adeleye ya ce:

"Mun kama wani adadi na maharan da suka aikata ta'addanci a Cocin St Francis Catholic Church dake garin Owo. Mun kwato motar da suka yi amfani da ita bayan harin, haka nan mun gano wasu makamai."

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

"Lokacin da suka kai harin sun je ne a kan Mashina amma da zasu tsere suka kwace wata Motar Golf. Mun yi nasarar kwato motar kuma ba da jimawa ba zamu cafke makasan baki ɗaya."

A wani labarin kuma Wani Jirgin sama ɗauke da mutane sama da 100 ya kama da wuta yayin sauka

Wani Jirgin sama da ya samu matsala yayin sauka ya kama da wuta a filin Jiragen sama na birnin Miami da ke ƙasar Amurka

Wani bidiyo ya nuna yadda Fasinjojin cikin jirgin ke ihun neman taimaki yayin da suke rige-rigen fitowa daga cikin jirgin saman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel