Katsina: Yan Sanda Da Yan Bijilante Sun Aike Da Wasu Yan Ta'adda Barzahu Bayan Tafka Gumurzu

Katsina: Yan Sanda Da Yan Bijilante Sun Aike Da Wasu Yan Ta'adda Barzahu Bayan Tafka Gumurzu

  • Jami'an yan sandan Najeriya da yan bijilante a karamar hukumar Safana ta Jihar Katsina sun kashe yan ta'adda biyu a Sabon Dawa
  • Mai magana da yawun yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da hakan yana mai cewa sun yi musayar wuta a yammacin ranar Talata
  • Kwamishinan yan sandan Kastina, Idrisu Dauda, ya yaba wa yan sandan da yan bijilante da mutanen garin bisa jarumta da jajircewa ya kuma yi alkawarin yan sanda za su cigaba da jajircewa wurin aikinsu

Katsina - Tawagar hadin gwiwa da ta kunshi rundunar yan sandan Najeriya da yan bijilante a karamar hukumar Safana ta Jihar Katsina sun kashe yan ta'adda biyu yayin musayar wuta a kauyen Sabon Dawa.

A cewar kakakin yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Laraba, ya ce an yi musayar wutan ne a yammacin ranar Talata, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Umurci Mawaki Portable Ya Kai Kansa Ofishinta Ko Ta Kamo Shi

Kwamishinan Yan Sandan Katsina.
Yan Sanda Da Yan Bijilante Sun Aike Da Wasu Yan Ta'adda Barzahu A Katsina. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Isah ya yi bayanin cewa:

"A ranar 21 ga watan Yunin 2021 misalin karfe 5 na yamma, an samu kiran neman dauki cewa yan ta'adda masu yawa, dauke da AK-47 sun kai hari kauyen Sabon Dawa, Yankin Zakka, Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina.
"DPO na Safana ya jagoranci tawagar yan sanda da bijilante a yankin, suka yi musayar wuta da yan ta'addan, suka kashe biyu cikinsu sannan suka dakile harin da suka yi nufin kai wa."

Kwamishinan yan sanda ya yi martani

Kwamishinan yan sandan Jihar Katsina, Idrisu Dauda, a martaninsa, ya yabawa tawagar jami'an tsaron da mutanen garin saboda juriyarsu da cewa 'sun daure sun kare garinsu daga harin yan ta'addan.'

Ya bada tabbacin cewa rundunar yan sanda za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaro a garurunsu'.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

Dauda ya bukaci mazauna garin su kira yan sandan a wadannan lambobin 08156977777 da 09053872247 don yin rahoton wani mutum ko mutane da ba su gamsu da su ba.

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel