Majalisar Dattawa ta sa ranar fara tantance sabbin Ministoci 7 da Buhari ya naɗa

Majalisar Dattawa ta sa ranar fara tantance sabbin Ministoci 7 da Buhari ya naɗa

  • Majalisar Dattawan tarayyan Najeriya ta ce zata tantance sabbin ministocin da shugaba Buhari ya aike mata a mako mai zuwa
  • Shugaban majalisar, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, wanda ya sanar da haka ya ce zasu tantance mutanen ne ranar Laraba mai zuwa
  • A ranar 15 ga watan Yuni, 2022, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tura wa majalisar sunayen sabbin ministocin domin amincewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta ce mako mai zuwa zata fara aikin tantance mutum Bakwai da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike mata da nufin naɗa su Ministoci.

PM News ta rahoto cewa shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Ahmad Lawan, ya ce ranar Laraba ta mako mai zuwa zasu tantance sabbin ministocin.

Majalisar dattawa ta kasa.
Majalisar Dattawa ta sa ranar fara tantance sabbin Ministoci 7 da Buhari ya naɗa Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Lawan ya sanar da haka ne a yau Laraba 22 ga watan Yuni, jim kaɗan kafin majalisar ta ɗage zamanta.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci, ya aika sunayen majalisa don tabbatar da su

"Zamu tantance sabbin ministocin da aka naɗa ranar Laraba ta mako mai zuwa," inji shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yaushe shugaban ƙasa ya aika sabbin ministocin?

Shugaban ƙasa Buhari, a wata wasika mai kwanan watan 15 ga watan Yuni, 2022, ya bukaci majalisar dattawa ta amince da mutum Bakwai da yake son naɗawa Ministoci.

A cewar Buhari, ya nemi sahalewar majalisar ne domin biyayya ga sashi na 147 (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 wanda aka yi wa garambawul.

Mutanen da shugaban ya tura domin tantancewa sun haɗa da, Henry Ikechukwu Ikoh daga jihar Abiya; Umana Okon Umana daga jihar Akwa Ibom; Ekumankama Joseph daga jihar Ebonyi; da Goodluck Nanah Opiah daga Imo.

Sauran kuma sune, Umar Ibrahim El-Yakub daga jihar Kano, Ademola Adewole Adegoroye daga jihar Ondo, da kuma Odum Udi daga jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani

Legit.ng Hausa ta gano cewa majalisar dattawa zata tantance mutanen ne ɗaya bayan ɗaya a zamanta na ranar ta Laraba.

A wani labarin kuma Karya ta kare, Kotu ta ɗaure wasu mutum biyu shekara 10 bisa 'Sihirin ninka kuɗi' a Sokoto

Kotu ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin zaman gidan Yari na shekara 10 bayan kama su da laifin "Sihirin ninka kudi' a Sokoto.

Mutanen biyu, Ibrahim Yakubu da Yakubu Ibrahim, sun gamsar da masu shigar da ƙara cewa suna iya ninka musu kudi, suka karɓi miliyoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel