Kotu ta ɗaure wasu mutum biyu saboda 'Sihirin ninka kuɗi' a Sokoto

Kotu ta ɗaure wasu mutum biyu saboda 'Sihirin ninka kuɗi' a Sokoto

  • Kotu ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin zaman gidan Yari na shekara 10 bayan kama su da laifin "Sihirin ninka kudi' a Sokoto
  • Mutanen biyu, Ibrahim Yakubu da Yakubu Ibrahim, sun gamsar da masu shigar da ƙara cewa suna iya ninka musu kudi, suka karɓi miliyoyi
  • Alƙalin babbar Kotun jihar Sokoto, Mai Shari'a Sifawa, ya umarci su maida kuɗin kuma a lalata kayayyakin da suke amfani da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Alƙalin babbar Kotun jihar Sakkwato, Mai shari'a Muhammad Sifawa, ya yanke wa wasu mutum biyu, Ibrahim Yakubu, da Yakubu Ibrahim, hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekara 10 kowannen su.

An yanke wa mutanen biyu wannan hukunci ne bayan kama su da laifin damfara da mallakar kuɗi sama da miliyan N5m ta hanyar ikirarin ƙarya.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa wato EFCC ta fitar a shafinta da tuwita da safiyar Laraba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun tada bama-bamai a wata babbar Kasuwa mutane na tsaka da harkokinsu

Yakubu Ibrahim da Ibrahim Yakubu.
Kotu ta ɗaure wasu mutum biyu saboda 'Sihirin ninka kuɗi' a Sokoto Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Sanarwan ta ce mutanen biyu da nufin damfara, suka gabatar wa masu kara da kan su cewa suna da ƙarfin ikon ninka kuɗi ko nawa ne ta hanyar kiran 'Juju' don haka suka karɓi kuɗi miliyan N5,612,000 daga hannun su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan laifin ya saɓa wa sashi na 310 na kundin dokokin Fenal na jihar Sokoto 2019 kuma an tanadi hukuncinsa a sashi na 311," a cewar sanarwan EFCC.

Shin mutanen sun amsa laifin su?

Mutanen biyu, Uba da ɗansa, sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi nan take. Lauyan masu ƙara, S.H Sa'ad, ya roki Kotu ta tabbatar tare da yanke musu hukuncin da ya dace.

Mai Shari'a Sifawa ya nuna gamsuwa da hujjojin ɓangaren masu ƙara kuma ya yanke wa waɗan da ake kara hukuncin zaman gidan Yari tsawon shekara 10 kowannen su.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kotu ta yanke wa Miji hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya kashe kwarton matarsa

Ko ya Kotu ta yi da miliyoyin da mutanen suka karɓa?

Haka nan kuma Alƙalin Kotu ya umarci mutanen biyu su maida wa waɗan da suka damfara kuɗaɗen su ta hannun hukumar EFCC.

Alkalin ya ƙara da umartan hukumar EFCC ta lalata kayan aikin da masu sihirin ke amfani da shi wajen aikata laifin.

A wani labarin na daban kuma 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar babban jigon APC ɗan takara a 2023

Myagun yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun sace mah a ifiyar ɗan takarar Sanatan Jigawa ta tsakiya a garin Kiyawa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Shisu, ya ce tuni kwamishina ya haɗa tawagar dakaru na musamman don ceto matar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel