Buhari: Tausayin Talaka ya sa na ki biyewa masu bada shawarar janye tallafin man fetur

Buhari: Tausayin Talaka ya sa na ki biyewa masu bada shawarar janye tallafin man fetur

  • Muhammadu Buhari ya yi wa kansa Lauya a kan matakinsa na kin janye kudin tallafin man fetur
  • Shugaban na Najeriya ya ce a yau har kasashen Yamma sun fara daukar nauyin biyan tallafin fetur
  • Buhari yake cewa babu dalilin da zai dauki matakin da zai kara jefa al’ummarsa a cikin wahala

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mai girma Muhammadu Buhari ya kare kan shi a kan matakin da ya dauka na kin janye tallafin man fetur kamar yadda masana su ka bada shawara.

Daily Trust ta ce irinsu bankin Duniya da hukumar bada lamuni ta Duniya ta nemi gwamnatin Najeriya ta daina biyan kudin tallafin mai, amma ta ki.

Da Shugaban na Najeriya ya yi hira da Bloomberg, ya bayyana dalilinsa na cigaba da kashe biliyoyin kudi domin ganin man fetur bai kara tsada ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

A cewar Shugaba Buhari, wadanda suka biyewa shawarar manyan yammacin Duniya su na yabawa aya zaki a dalilin tsare-tsarensu da suka dauko.

Ba a nan take ba - Buhari

Buhari yake cewa tsarin yana da kyau a rubuce, amma idan aka aikata, za a bar mutane a wahala.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mafi yawan kasashen yammacin Duniya su na biyan tallafin man fetur a yau. Me zai sa mu cire na mu. Ai duk jirgi daya ya dauko mu.”
“Manyan Yamma su na daukar darasi a aikace. Tsarin da yake kan takarda ya sha ban-bam da abin da za a gani a kasa idan an aiwatar da shi.”
Buhari
Shugaban Najeriya Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Gwamnatina ta yi shirin cire tallafin a karshen bara. Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da ganin abin da ya faru, abin bai yiwu ba.”

- Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori

Abubuwa za su gyaru a Najeriya

An rahoto shugaban kasar yana cewa idan aka gyara matatun kasar za a samu sauki, haka zalika matatun Dangote, BUA da Waltersmith za su fara yin aiki.

Buhari ya yi maganar yadda ake samun rashin tabbas na kudin waje, wanda hakan yake taba tattali.

Idan aka fara tace mai a Najeriya sannan ana noma abincin da za a ci, Buhari yana ganin farashin kaya za su yi kasam sannan kuma a samu zaman lafiya.

An rasa mutum 3000 a watanni 6

Kun samu rahoto cewa lissafin Nigeria Security Tracker ya nuna an hallaka mutum kusan 3500 a cikin kwanaki 195 a Najeriya a dalilin matsalar rashin tsaro.

Alkaluman Nigeria Security Tracker na nufin a kowace rana, sai mutum 17 sun bakunci barzahu. Haka kuma an yi garkuwa da mutane fiye da 2, 000 a kasar nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel