Masu Garkuwa Sun Sace Tsohon Sakataren Hukumar NFF, Sani Toro

Masu Garkuwa Sun Sace Tsohon Sakataren Hukumar NFF, Sani Toro

  • Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace tsohon sakatern NFF, Mr Sani Toro
  • An sace Toro ne a hanyarsa na kowama gidansa da ke Bauchi daga birnin taraya Abuja inda ta tafi daurin auren dan Aminu Maigari
  • Kakakin yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar da sace shi, amma ya ce ba shi da cikakken bayanin tunda abin ba a Bauchi ya faru ba

Yan bindiga sun sace tsohon sakataren Hukumar Ƙwallon Kafa Ta Najeriya, NFF, Sani Toro, Premium Times ta rahoto.

An sace tsohon sakataren na NFF ne a hanyarsa ta komawa Bauchi daga Abuja inda ya hallarci daurin auren dan tsohon shugaban NFF Aminu Maigari.

Sani Toro.
Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Tsohon Sakataren NFF, Sani Toro. Hoto: @PremiumTimesNg
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

EFCC: Yan Najeriya Sun Dena Kazar-kazar Wurin Tona Asirin Masu 'Sata' Duk La'ada Mai Tsoka Da Muke Basu

Yan sanda sun yi martani kan lamarin

Kakakin yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar wa Premium Times sace shin, amma ya ce ba shi da cikakken bayanin tunda abin ba a Bauchi ya faru ba.

"Eh, labarin gaskiya ne. Na yi magana da ɗaya cikin yayansa, wanda ya fada min cewa an sace shi ni kusa da hanyar Akwanga a Nasarawa yayin da ya ke dawowa daga Abuja. Idan na samu karin bayani zan sanar da ku," in ji Mr Wakil.

An rahoto cewa an sace Mr Toro ne tare da tsohon mataimakin kocin Super Eagles, Garba Yila.

Kawo yanzu ba a san wanda suka sace shi ba kuma ba su riga sun tuntubi yan uwansa don neman kudin fansa ba.

Garkuwa da mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a wasu jihohin Najeriya kuma kungiyoyin yan bindiga daban-daban ke aikata abin.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan ta'adda sun harba bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.

Asali: Legit.ng

Online view pixel