Harin Kwantar Bauna: Yan Ta'adda Sun Kashe Manjo Na Soja, Sun Kona Motar Sojoji Sun Sace Makamai a Niger

Harin Kwantar Bauna: Yan Ta'adda Sun Kashe Manjo Na Soja, Sun Kona Motar Sojoji Sun Sace Makamai a Niger

  • Yan ta'adda sun afka wa tawagar motoccin sojoji a karamar hukumar Mariga ta Jihar Niger a ranar Laraba sun kashe soja daya mai mukamin manjo
  • A harin kwantar baunar, yan ta'addan sun kuma raunta wasu sojojin sannan an nemi wani soja guda a an rasa
  • Majiya daga rundunar sojoji da ta tabbatar da afkuwar lamarin ta ce kuma ce yan ta'addan sun kona motar sojoji sun kuma sace makamai

Jihar Niger - An kashe wani jami'in soja mai mukamin manjo a wani hari da yan ta'adda suka kai wa tawagar motoccin sojoji a karamar hukumar Mariga ta Jihar Niger.

Majiyoyi daga rundunar sojoji wadanda suke da masaniya kan lamarin sun shaida wa Premium Times cewa tawagar ta Makarantar Sojoji (NMS) ne da Sashin Bada Horaswa na Sojoji (TRADOC).

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan ta'adda sun harba bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Taswirar Jihar Niger.
Yan Ta'adda Sun Kashe Manjo Na Soja, Sun Kona Motar Sojoji Sun Sace Makamai a Niger. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Lamarin, wanda ya faru a ranar Laraba ya afku ne a kusa da kauyen Rijiyan Daji a karamar hukumar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin hada wannan rahoton, an nemi wani jami'in soja daya ba a gan shi ba yayin da wasu uku suka raunta sakamakon musayar wuta da yan ta'addan.

Sojan da ya rasu, yana da rai bayan harin, amma ya ce ga garin ku bayan an garzaya da shi wani asibiti da ke Kontagora, wata karamar hukuma a jihar.

Baya ga rasa rai da aka yi, yan ta'addan sun kona wata mota kirar Toyota Hilux na sojojin kuma sun tsere da makamai.

An baza sojoji nemo wanda ba a gani ba

Majiyar ta kuma ce a an baza tawaga domin nemo da ceto jami'in sojan da ba a gani ba.

An yi kokarin ji ta bakin kakakin rundunar sojoji, Onyema Nwachukwu kan lamarin amma hakan bai yi wu ba.

Kara karanta wannan

Borno: Hotunan Tubabbun 'Yan Boko Haram 204 Yayin da Suka Mika Kansu ga Sojoji

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel