A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro - Buhari

A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro - Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu a kan matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar nan
  • Buhari ya bayyana cewa a kullum yana rayuwa cikin damuwa da bakin ciki saboda wannan kalubale na tsaro da ya yiwa kasar katutu
  • Ya yi kira ga al'ummar Najeriya da su dage da addu'o'i tare da ba hukumomin tsaro hadin kai domin kawo karshen wannan lamari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a kasar Najeriya.

Buhari ya kuma roki yan Najeriya da su dage da addu’a a kan ranshin tsaro a cikin jawabinsa na ranar Damokradiyya ta 2022 da ya yiwa yan kasar a Abuja, jaridar Independent ta rahoto.

A cewarsa, gwamnatin na aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro a kasar nan, jaridar The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Buratai: Yadda Za a Kawo Karshen Kallubalen Tsaro a Najeriya

A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro - Buhari
A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro - Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Don cimma wannan, dole sai dukkanmu mun bayar da gudunmawa. Ba aiki gwamnati bane ita kadai. Ina bukatar dukkanin al’ummar kasar da su taimaka sannan su ba hukumomin tsaronmu hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abun da basu yarda da shi ba ga hukumomin tsaro. Za mu samu kasa mai tsaro ne kawai idan muka yi nasarar hana laifuka bawai bayan an aikata laifi ba.
“A wannan rana ta musamman, ina so dukkanmu mu sanya wadanda ayyukan ta’addanci ya ritsa da su a zukatanmu da addu’o’inmu. A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda wadannan mutane da wadanda ke garkame sakamakon ta’addanci da garkuwa da mutane. Ni da hukumomin tsaro muna yin duk mai yiwuwa don kubutar da wadannan maza da matan cikin koshin lafiya.
“Ga wadanda suka rasa rayukansu, za mu ci gaba da nema ma iyalansu adalci a kan makasan. Ga wadanda ke tsare a yanzu haka, ba za mu daina ba har sai an sako su, kuma a gurfanar da wadanda suka yi garkuwa da su. Idan duk muka hada kanmu, za mu yi nasara a kan masu ta’addanci da barna.”

Kara karanta wannan

Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gyara wasu tsare-tsaren tsaro na kasar.

Ya ce:

“Wasu daga cikin kadarorin tsaro da muka sayo shekaru uku da suka gabata sun iso kuma an tura su wurare. Ana habbaka tsarin tsaro na yanar gizo da tsarin sa ido don kara habbaka ikon mu na bin diddigin masu aikata laifuka. Muna kuma daukar sabbin ma’aikata da horar da su a dukkan hukumomin tsaro da na leken asiri domin karfafa tsaron kasar baki daya.”

Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi na musamman gobe Lahadi

A baya mun kawo cewa, Shugaba Muhammadu Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi ta musamman misalin karfe 7 na safiyar Lahadi, 12 ga watan Yuni, 2022.

Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya bayyana hakan yayin hira da yan gidan rediyo ranar Alhamis a Abuja.

Lai Mohammed yace zai yi jawabin bisa murnar ranar demokradiyya ta shekarar nan.

Kara karanta wannan

Rikici: Gwamnan Fintiri ya saka dokar hana fita a kananan hukumomi biyu na jiharsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel