Buratai: Yadda Za a Kawo Karshen Kallubalen Tsaro a Najeriya

Buratai: Yadda Za a Kawo Karshen Kallubalen Tsaro a Najeriya

  • Tukur Buratai, Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya ya bayyana hanyoyin da za a kawo karshen rashin tsaro a Najeriya
  • Buratai ya yi wannan jawabin ne a wurin wani taro na rana daya da aka yi a birnin tarayya Abuja domin gano hanyoyin samar da tsaro a Najeriya
  • Jakadan na Najeriya a Jamhuriyar Benin ya ce dole gwamnati ta aiwatar da wani tsari da kowanne dan kasa zai taka rawa a harkar tsaro

FCT, Abuja - Jakadar Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanat Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya bayyana hanyoyin da za a bi don kawo karshen rashin tsaro, yana mai cewa kowa na da rawar da zai taka don kawo tsaro.

Buratai, tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasan Najeriya, ya yi magana a ranar Asabar a wani taron tsaro da aka yi na rana daya Arewa House a Abuja.

Kara karanta wannan

An jikkata wasu da dama yayin da rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo

Buratai: Yadda Za a Kawo Karshen Kallubalen Tsaro a Najeriya
Buratai Ya Bayyana Hanyoyin Da Za A Bi A Kawo Karshen Rashin Tsaro a Najeriya. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a halin yanzu akwai kallubalen tsaro da dama a sassan kasar kamar ta'addanci a arewa maso gabas, yan bindiga da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, satar danyen mai da neman ballewa daga kasa a kudu maso kudu.

Hanyoyin da za a bi domin magance kallubalen tsaro a Najeriya, Buratai

Buratai ya bada shawarar cewa dole a yi amfani da tsarin da kowanne dan kasa zai taka muhimmin rawa wurin magance kallubalen tsaro kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya yi bayanin cewa tsarin ya kunshi masu ruwa da tsaki daga cikin al'umma, kamar shugabannin addini, matasa, malamai, mata, kungiyoyin al'umma, kafafen watsa labarai, jami'an tsaro da tattara bayanan sirri.

"Akwai bukatar a rika wayar da kan al'umma kan rawar da za su taka wurin samar da tsaro a kasar ta hanyar hukumomin kamar Ma'aikatan Wayar Da Kan Al'umma, NOA, da sauransu," in ji shi.

Kara karanta wannan

PDP: Tsohon Ministan Jonathan Ya Ci Zaben Fidda Gwanni Na Sanata a Jigawa

Buratai ya kuma ce akwai bukatar a farfado da kamfanin kera makamai na DICON don magance kallubalen rashin isasun makamai da sojojin Najeriya ke fama da shi.

"Wannan na da muhimmanci domin cike gibin karancin makamai da sojojin Najeriya ke fama da shi da sabbin barazana.
"Don cimma hakan, Ma'aikatar Tsaro, tare da hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki za su iya hada hannu don samar da kayan horaswa ga ma'aikatan DICON.
"Hakan zai kara kwarewarsu da makamai da za su kera wa sojojin Najeriya," in ji shi.

Buratai ya kara da cewa garambawul da ake yi wa rundunar yan sandan Najeriya, siyo sabbin na'urorin tattara bayanan sirri da tsare iyakokin Najeriya zai taimaka sosai wurin samar da tsaro a kasar.

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

A wani rahoton, yan sanda a Abuja a safiyar ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022, sun ceto mutane hudu daga mabuyar masu garkuwa a Dutsen Dudu a unguwar Kuje sun kuma lalata maboyar yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Bada Hutun Ranar Demokradiyya Na 2022

Rundunar yan sandan ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel