Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Bayan nasarar da ya samu a kwanan baya a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ga jerin ajandoji guda bakwai na Asiwaju Bola Tinubu.

Tinubu, wanda ya samu kuri’u 1,271, ya doke wasu mutum 13 a zaben. Babban abokin hamayyarsa shine tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya samu kuri'u 316.

Burin nasa na gaje Buhari ya samu tasgaron 'yan adawa daga wasu mukarrabansa da suka hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda ya samu kuri’u 235.

Ajandoji 7 na Osinbajo
Burin Tinubu: Ajanda 7 da dan takarar APC Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: Depositphotos

Ga jerin ajandojinsa ga kasar idan aka zabe shi a 2023 a cewar PM News.

1. Shugabanci

Samar da shugabanci na sauyi mai kyau wanda zai hada kan 'yan Najeriya baki daya kuma ya kai kasar ga cimma manufa da hangen nesa nagari.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Fasaha

Yin amfani da fasahar zamani don kawo sauyin tafiya daidai da zamani da habakar tattalin arzikin kasa.

3. Tsaro

Kirkirar yanayin da zai ba 'yan ƙasa damar sakewa da yin mu'amala cikin 'yanci a cikin kasar.

4. More rayuwa

Kawo babban ci gaban ababen more rayuwa ta hanyar gina muhimman ayyuka (sa'o'i 24 na samun wutar lantarki, hanyoyi, gadoji da dai sauransu) wadanda za su hada kasa tare da habaka ingancin rayuwa.

5. Kasuwancin cikin gida

Gina tsarin da ke ba da daman karfafa kasuwancin cikin gida don habaka gasa mai kyau da gogayya da kasuwannin duniya.

6. Ilimi

Kaddamar da abubuwan da za su habaka ilimi da kuma ba dalibai a kowane rukuni dabarun damawa da bukatar zamani da duniya.

Yadawa da kawo dabaru da ka iya inganta alfaharin farkar da 'yan Najeriya ga kishin kasa.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

7. Demokradiyya

Habaka mulkin demokradiyya, fahimtar hazakar dan adam da samar da yanayi don wadata da ci gaba.

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

A wani labarin, kungiyar yakin neman zaben Yahaya Bello na neman shugaban kasa ta caccaki fitowar Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Punch ta ruwaito.

Sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni mai taken, ‘Yahaya Bello ne dai gwarzon wadanda aka zalunta.'

A cikin sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Yemi Kolapo, ya fitar kuma Legit.ng ta gani, ya bayyana atisayen zaben fidda gwnain APC a matsayin wani tsari da aka samu matsala a cikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel