Kungiyar Ansaru ta musanta hannu a satar fasinjojin jirgin kasa, ta ce aikin Allah take

Kungiyar Ansaru ta musanta hannu a satar fasinjojin jirgin kasa, ta ce aikin Allah take

  • Kungiyar a'addanci ta Ansaru ta barranta kanta da farmakin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris
  • A wata takarda da ansaru ta raba wa fasinjoji kan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua, ta ce ta kare Musulmai da Musulunci ta ke yi
  • A takardar, kungiyar ta ce babu wani Abu Barra da ke shugabantar ta, amma za ta sanar da sunan shugabanta nan babu dadewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kungiyar ta'addanci ta Jamar Ansarul Muslimina fi Biladi Sudan wacce aka fi sani da Ansaru sun musanta ka farmaki kan jirgn kasan da ya kwaso fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022, inda rayuka 9 suka salwanta.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a wata takaa da ta rarrabawa matafiya kan babban titin Birnin-Gwari zuwa Funtua a yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

Batun mika Kyari Amurka: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan makomar Abba Kyari

Kungiyar Ansaru ta musanta hannu a satar fasinjojin jirgin kasa, ta ce aikin Allah take
Kungiyar Ansaru ta musanta hannu a satar fasinjojin jirgin kasa, ta ce aikin Allah take. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

Takardar mai taken: "Sako ga gwamnatin Najerya da 'yan kasa" an rubuta da Hausa kuma kwafin da Daily Trust ta samu ya ce kai wa 'yan kasa marasa laifi farmaki ba shi daga cikin tsarikansu.

Kama yadda kungiyar ta ce, babban burninsu shi ne kare Musulunci da Musulmai wadanda aka cuta ko kuma aka matsantawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta kara da ikirarin cewa, wani mutum mai suna Abu Barra ba shi bane shugabansu inda suka kara da cewa za su sanar wa duniya shugabansu nan babu dadewa.

Sun kara da cewa, burinsu da manufar su ita ce kare Musulunci daga "muguwar gwamnatin Najeriya tare da sauran kasashen bakake na Afrika."

Wani shugaban matasa daga Birnin Gwari wanda ya bukaci boye sunansa, ya sanar da Daily Trust cewa kungiyar ta fito ana tsaka domin rarrabe takardar ga masu ababen hawa da ke wucewa.

Kara karanta wannan

An kuma: Mummunan fashewa ta auku a Kano an rasa shaguna, mutum 20 sun jikkata

"Ba su kai wa kowa farmaki a kan hanya ba. Kawai mika takardun suka dinga yi ga direbobin motocin haya kan babban titin Birnin Gwari," yace.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata wallafa a shafinsa na Facebook na ranar 17 ga watan Afirilu, wani da ake zargin 'dan kungiyar Ansaru ne, ya soki rahoton da ke yawo mai alakanta harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da kungiyar.

Hakazalika, wani 'dan jarida mai yawan kawo rahotanni kan kalubalen tsaro na arewa maso yamma, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce akwai tantama idan Ansaru ce ta kai farmaki kan jirgin kasan.

"Batun 'ya'yansu da aka dauke daga Nasarawa da kuma yanayin yaren da suke yin amfani da shi da muryoyin maharan da aka nada a hirar waya ya fi kama da na 'yan ta'addan Darul salam a maimakon Ansaru ko Boko Haram," yace.

Karin bayani: Ɗan Ango Abdullahi, 'yar ajinsu Osinbajo sun yi magana a sabon bidiyon da ƴan ta'adda suka saki

Kara karanta wannan

Neman Kafa Shari'a: CAN Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kama Wasu Malaman Addinin Musulunci a Taraba

A wani labari na daban, 'yan ta'addan da suka sace fasinjojin da ke jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris din 2022, sun sake sakin sabon bidiyon wadanda suka sace.

Wani jirgin kasa da ya doshi Kaduna daga Abuja ya zo karkashin farmakin 'yan ta'adda, kasa da mintuna 20 kafin isar sa Rigasa.

A yayin da suka harbe fasinjoji tara kuma suka mutu a take, sun sace sama da fasinjoji 60 da suka hada da yara kanana da tsofaffi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel