Karin bayani: Ɗan Ango Abdullahi, 'yar ajinsu Osinbajo sun yi magana a sabon bidiyon da ƴan ta'adda suka saki

Karin bayani: Ɗan Ango Abdullahi, 'yar ajinsu Osinbajo sun yi magana a sabon bidiyon da ƴan ta'adda suka saki

  • 'Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun saki sabon bidiyon wadanda ke hannunsu
  • A bidiyon, Sadiq Ango Abdullahi ya yi magana inda kuma aka ga wani 'yar ajinsu Osinbajo yana rokon FG
  • 'Yan ta'addan na bukatar a sako 'ya'yansu takwas da FG ta kwashe tare da wasu kwamandojinsu da aka kama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

'Yan ta'addan da suka sace fasinjojin da ke jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris din 2022, sun sake sakin sabon bidiyon wadanda suka sace.

Wani jirgin kasa da ya doshi Kaduna daga Abuja ya zo karkashin farmakin 'yan ta'adda, kasa da mintuna 20 kafin isar sa Rigasa.

Da Ɗuminsa: Ɗan Ango Abdullahi, 'yar ajinsu Osinbajo sun yi magana a sabon bidiyon da ƴan ta'adda suka saki
Da Ɗuminsa: Ɗan Ango Abdullahi, 'yar ajinsu Osinbajo sun yi magana a sabon bidiyon da ƴan ta'adda suka saki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da suka harbe fasinjoji tara kuma suka mutu a take, sun sace sama da fasinjoji 60 da suka hada da yara kanana da tsofaffi.

Kara karanta wannan

Jirgin Abuja-Kaduna: Yan bindigan da suka sace Fasinjojin jirgi sun saki sabon Bidiyo, sun ba FG zaɓi biyu

'Yan ta'addan sun dinga sakin jerin bidiyoyi na wadanda suka sace.

A daya daga cikin bidiyoyin, sun yi barazanar halaka wadanda suka sace idan gwamnatin tarayya ta gaza cika sharuddansu wanda suka ce sai an sako 'ya'yansu da wasu kwamandojinsu.

A sabon bidiyon, takwas daga cikin fasinjojin wadanda suka hada da maza biyar da mata uku, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta karba bukatar 'yan ta'addan, Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da mazan ke gurfane a kan guiwoyinsu, matan sun zauna kusa da su a kan tabarma.

Wani dan bindiga wanda ya bayyana a bidiyon ya ce gwamnati za ta iya sauraron wadanda suka kama ko kuma su yi watsi da su.

Sadiq, 'dan dattijon arewa, Ango Abdullahi, ya ce da yawa daga cikin su na su da lafiya.

"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo mana dauki. Kwanan mu 62 a nan. Da yawa daga cikin mu babu lafiya kuma ba ma cikin hali maai kyau kuma a kowacce rana kara munana lamarin ya ke. Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo mana dauki kafin mu fara rasa rayukan mu," yace.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji

Wata daga cikin wadanda ke hannun 'yan bindigan wacce tsohuwar 'yar ajinsu Farfesa Yemi Osinbajo ce a makarantar koyon shari'a, ta fashe da kuma inda ta ce tana tunanin makomar dan ta Wanda sikila ne.

"Suna na Gladys... Ina kira ga Farfesa Yemi Osinbajo wanda muka zauna aji daya a 78/79 a makarantar koyon shari'a. Kai kaka ne kuma uba, ka kawo mana dauki saboda kwanan mu 62 a nan kuma ina da 'da sikila. Ban san halin da ya ke ciki ba."
"Ina kira ga gwamnatin tarayya da Rotimi Amaechi wanda ministan sufuri ne da ya taimaka mana. Ina roko, dukkanmu ba mu da lafiya. Amma 'da na da ke fama da cutar sikila, ban san halin da ya ke ciki ba. Ina kira ga gwamnatin tarayya," ta ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel