Batun mika Kyari Amurka: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan makomar Abba Kyari

Batun mika Kyari Amurka: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan makomar Abba Kyari

  • Kotu ta sanya ranar da za a ji batun Abba Kyari kan yiwuwar mika shi Amurka ko ci gaba da zamansa a Najeriya
  • Kasar Amurka dai a baya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta mika Kyari domin gurfanar dashi a gaban kotu
  • Wannan na zuwa ne bayan da wani bincike yace Kyari na da hannu a wata damfara da Hushpuppi ya yi a 2020

FCT, Abuja - Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun Abuja, ya sanya ranar 29 ga watan Agusta domin yanke hukunci kan karar da ke neman tasa keyar DCP, Abba Kyari zuwa kasar Amurka domin yi masa shari’a kan wata damfara da ake zargin da hannunsa.

Ana zargin Abba Kyari da kulla harkalla da wani kasurgumin dan damfara, Abbas Roman (Huspuppi) da ke barnarsa a duniya, lamarin ya kuma ba 'yan Najeriya da dama mamaki.

Kara karanta wannan

Balo-balo: Abba Kyari ya tono batutuwa, ya fadi gaskiyar alakarsa da Hushpuppi

A ci gaba da jin batutuwan neman mika shi waje, alkalin ya tsayar da ranar ne bayan sauraran hujjoji akan karar da bangarorin da abin ya shafa suka bijiro dasu, rahoton Punch.

Kotu za ta duba yiwuwar tasa keyar Abba Kyari kasar Amurka
Shari'ar Kyari a Amurka: An sanya ranar da Abba Kyari zai san matsayarsa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ba daidai bane mika Kyari kasar Amurka, inji Lauyansa

Kyari wanda wani babban Lauyan Najeriya (SAN), Nureni Jimoh ya wakilci bayanansa, ya roki kotun da ta ki amincewa da bukatar mika shi Amurka bisa hujjar cewa bai aikata laifin da zai sa gwamnatin tarayya ta kai shi kasar Amurka ba da sunan hukunta shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kyari ya sanar da kotun cewa fiye da shekara guda kafin a kama shi, ya rubuta wa AGF Abubakar Malami da Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba wasika, inda ya sanar da su cewa ya bude sahar sadarwa da wanda ake zargin dan damfara ne, Ramon Abass.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu za ta ci gaba da sauraran batun mika Abba Kyari Amurka

A cikin wasiku guda biyu da aka mika a gaban kotu, Kyari ya bayyana cewa, manufar alakarsu ba komai bane face a baiwa Hushpuppi kwarin gwiwa da kuma jawo shi zuwa Najeriya inda tuni rundunarsa ke shirye don kwamushe shi.

Ban da haka, ya sanar da kotun cewa hukumomin Amurka sun taba yaba masa bisa jajircewar da yake nunawa wajen yaki da 'yan damfarar yanar gizo, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Ya kuma shaida wa kotun cewa tuhumar da ake masa na damfara da gwamnatin Amurka ta yi, ba laifi ba ne a karkashin dokar mike mutum waje, don haka bai kamata kotu ta bari a yi amfani da wannan lamari don mika shi Amurka ba.

Lauyan gwamnatin tarayya, Pius Akuta ya bukaci kotun da ta yi watsi da hujjojin wanda ake kara.

Ya ce gwamnatin Amurka ta cika sharuddan karbar Kyari bisa tuhumar da ake yi masa da kuma bukatar mika shi kasar domin fuskantar shari'a.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF

Balo-balo: Abba Kyari ya tono batutuwa, ya fadi gaskiyar alakarsa da Hushpuppi

A wani labarin, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ya yi zargin cewa matakin da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya dauka na mika shi kasar Amurka, ba shi da amfani ga shari’a, kana ya yi bayanin alakarsa da Hushpuppi.

A daya daga cikin sabbin kararrakin da aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, Kyari a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni, ya bukaci mai shari’a Inyang Ekwo da kada ya amince da tasa keyar sa zuwa Amurka domin fuskantar shari’a kan hannu a wata damfara.

Ya yi zargin cewa shirin mika shi Amurka domin gurfanar da shi ba komai bane face nufin hukunta shi, inji rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel