Karin bayani: Kotu za ta ci gaba da sauraran batun mika Abba Kyari Amurka

Karin bayani: Kotu za ta ci gaba da sauraran batun mika Abba Kyari Amurka

  • A yau ne wata babbar kotun tarayya ta bayyana ranar da za ta ci gaba da sauraran shari'ar mika Abba Kyari kasar Amurka
  • Ana zargin Abba Kyari ne da hannu a wata damfara da fitaccen dan damfarar yanar gizo; Hushpuppi ya yi a Qatar
  • Ana ta kai ruwa rana tun bayan da wata kotu a Amurka ta nemi gurfanar da dan sandan kan alakarsa da Hushpuppi

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sa ranar Juma’a za ta ci gaba da sauraren karar mika ACP Abba Kyari da aka dakatar zuwa hannun Amurka, The Nation ta ruwaito.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya zabi ranar ne a ranar Alhamis domin baiwa babban lauyan gwamnati damar shigar da kara a hukumance a kan batun da Kyari ya shigar na kin amincewa da matakin farko na kalubalantar cancantar mika shi da AGF ya shigar.

Kara karanta wannan

Balo-balo: Abba Kyari ya tono batutuwa, ya fadi gaskiyar alakarsa da Hushpuppi

Ranar Juma'a za a ci gaba da sauraran shari'ar mika Abba Kyari Amurka
Yanzu-Yanzu: Kotu za ta ci gaba da sauraran batun mika Abba Kyari Amurka | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

AGF ya nemi kotu ta ba ta izinin mika Kyari ga hukumomin Amurka dangane da alakarsa da wanda ake zargi da damfara ta yanar gizo, Abbas Ramon (wanda aka fi sani da Hushpuppi).

Baya ga wannan batu na damfara, idan baku manta ba Abba Kyari na fuskantar shari'a a Najeriya kan kulla harkallar kwaya da wasu mutane a kasashen waje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An nuna wasu hujjoji da ke nuna jami'in dan sandan na karbar cin hanci domin tabbatar da karbar wasu kayayyakin kwaya, kamar yadda a baya jaridar Punch ta ruwaito.

An gurfanar da shi a kotu, inda tuni aka tura Kyari magarkama domin ci gaba da jiran yadda za ta kaya a kotun.

Balo-balo: Abba Kyari ya tono batutuwa, ya fadi gaskiyar alakarsa da Hushpuppi

A gefe guda, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ya yi zargin cewa matakin da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya dauka na mika shi kasar Amurka, ba shi da amfani ga shari’a, kana ya yi bayanin alakarsa da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Ni masoyin Arewa ne, zan lallasa Atiku a 2023, 'yan Adamawa ni za su zaba, inji Okorocha

A daya daga cikin sabbin kararrakin da aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, Kyari a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni, ya bukaci mai shari’a Inyang Ekwo da kada ya amince da tasa keyar sa zuwa Amurka domin fuskantar shari’a kan hannu a wata damfara.

Ya yi zargin cewa shirin mika shi Amurka domin gurfanar da shi ba komai bane face nufin hukunta shi, inji rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel