Sojoji sun yi ram da bakon haure da ke kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a Sokoto, DHQ

Sojoji sun yi ram da bakon haure da ke kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a Sokoto, DHQ

  • Hedkwatar tsaro ta bayyana yadda rundunar sojin Najeriya ta Operation Hadarin Daji ta samu nasarar damke wani dan ta'addan bakon haure a Jihar Sokoto
  • Daraktan watsa labarun sojin, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya sanar da hakan a Abuja ga manema labarai yayin bayyana ayyukan sojoji tsakanin ranar 19 ga Mayu da 2 ga watan Yuni
  • Ya shaida yadda sojojin su ka samu nasarar halaka manyan 'yan ta'adda, ceto jama'a tare da kwace miyagun makamai har da dukiyoyi masu yawa daga wurinsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hedkwatar tsaro ta ce rundunar sojojin Najeriya ta operation Hadarin Daji a ranar 21 ga watan Mayu ta damke wani Jabe Buba, bakon haure kuma fitaccen mai kai wa 'yan ta'adda bayanai a kauyen Garuwa cikin karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto.

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya sanar da hakan yayin jawabi ga manema labarai kan nasarorin da sojojin suka samu tsakanin 19 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun bindige 'yan ta'adda 14, sun damke 15 tare da ceto iyalansu 100

Sojoji sun yi ram da bakon haure da ke kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a Sokoto, DHQ
Sojoji sun yi ram da bakon haure da ke kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a Sokoto, DHQ. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Onyeuko yace an samu hotuna da bidiyon bakon hauren yana rike da bindiga a daji a wayarsa kuma an samu N130,000 daga wurinsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya shaida yadda dakarun suka samo shanu 292 da rakumi daya yayin arangama da 'yan ta'addan a kauyen Dampo da ke karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Onyeuko ya ce rundunar ta samu nasarar ceto mutane 152 da aka yi garkuwa da su, ta kuma halaka 'yan bindiga 18 tare da kama wasu 25 cikin dan datsin.

Ya bayyana cewa sun samu nasarar kwace bindigogi hudu, kirar AK 47, carbin harsasai 100, shanu 458 da su ka sace da babura 20.

A cewarsa, Rundunar Operation Whirl Stroke ta samu nasarar halaka shugaban wata rundunar 'yan ta'adda da wasu mutane biyu da su ka sanya kayan sojoji a kan titin Zakibiam-Ugba da ke Jihar Binuwai tare da ceto mutum daya daga hannunsu.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

Kakakin rundunar sojin ya ce cikin abubuwan da aka kwato a hannunsu akwai AK 47 guda daya, carbin harsasai, mota kirar Toyota Corolla da kuma katin bankin wani Felix Terzenqwe.

Ya ce sun yi ram da wani fitinannen dan bindiga, Morris Ayitu tare da matarsa da abokin harkallarsa bayan sun kai samame gidansa da ke Abirisi a karamar hukumar Guma cikin Jihar Nasarawa.

Kamar yadda Onyeuko ya bayyana, Rundunar Operation Safe Haven, OPSH, a ranar 21 ga watan Mayu ta yaye 'yan sa kan guda 122 wadanda ta horar don su dinga taya jami'an tsaro tabbatar da tsaro a anguwanni daban-daban da ke karamar hukumar Sanga a Jihar Kaduna.

Hedkwatar OPSH ta Jihar Filato kuwa ta samu nasarar ganawa da jagororin Fulanin Bemood don tabbatar da tsaro a yankin Kuru da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

Zamfara: 'Yan bindiga sun sheƙe ƴan sa kai sama da 30 a Bunguɗu, sun sace shanu

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Rundunar soji ta magantu kan labarin barnar da 'yan ta'addan Kamaru suka yi a Najeriya

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a ranar Litinin sun halaka sama da 'yan sa kai 30 a wani artabun da suka yi kusa da yankin Gidan Dan Inna da ke Auki a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun kutsa gidan Inna tun farko kuma wasu sun kai farmaki kauyuka masu makwabtaka inda suka dinga satar shanu, Daily Trust ta ruwaito.

Sun harbe wasu mazauna yankin kuma sun tsere da shanunsu.

"Jim kadan bayan nan, shugabannin 'yan sa kai na a kalla yankuna 10 masu makwabtaka suka fara kiran mambobinsu inda suka bi sahun miyagun tare da kwato wasu shanun satan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel