Sojojin Najeriya sun bindige 'yan ta'adda 14, sun damke 15 tare da ceto iyalansu 100

Sojojin Najeriya sun bindige 'yan ta'adda 14, sun damke 15 tare da ceto iyalansu 100

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun bindige 'yan Boko Haram/ISWAP 14 tare da damke wasu 15 da ransu duk a jihar Borno
  • Kamar yadda Bernard Onyeuko ya sanar, dakarun sun kai samame maboyar 'yan ta'addan inda suka ceto iyalansu 100
  • Sun yi nasarar kwato miyagun makamai inda a halin yanzu suka mika su ga hukumomin da suka dace

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - A ranar Alhamis, hedkwatar tsaro ta kasa ta ce dakarun Operation Hadin Kai a makonni biyu da suka gabata sun halaka 'yan ta'adda 14 tare da damke wasu 15.

A yayin bayani ga manema labarai a Abuja, daraktan yada labaran tsaro, Bernard Onyeuko, ya ce wannan cigaban ya biyo bayan tsanantar ayyukan sojojin a yankin arewa maso gabas tsakanin 19 ga watan Mayu da 2 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

Sojojin Najeriya sun bindige 'yan ta'adda 14, sun damke 15 tare da ceto iyalansu 100
Sojojin Najeriya sun bindige 'yan ta'adda 14, sun damke 15 tare da ceto iyalansu 100. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Onyeuko ya ce iyalan 'yan ta'addan arewa maso gabas da suka hada da mata 33 da yara 67 duk an ceto su, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce dakarun sojin tare da hadin guiwar jami'an tsaro na farin kaya a ranar 22 ga watan Mayu sun matukar lallasa 'yan ta'adda a Amdaga, Balazola, Ndakaine, Jango, Sabah da Gobara duk a karamar hukumar Gwoza a Borno.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Onyeuko ya ce maboyar 'yan ta'addan Boko Haram da na ISWAP da ke yankin duk an mitsike su a yayin arangamar.

Ya kara da cewa, 'yan ta'addan sun tsere a firgice sakamakon ruwan wutar da suka ji dakarun sun sakar musu, kuma sai suka bar kadarorinsu da iyalansu.

Kakakin hukumar tsaro ya kara da cewa dakarun sun kara da samo wata motar aiki mallakin Hukumar kula da tituna ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

'An Kashe Kwamandan Boko Haram Da Mataimakinsa' Yayin Da Mafarautar Suka Yi Artabu Da 'Yan Ta'adda a Borno

Abun hawan kamar yadda yace, an sace shi a watan Fabrairun 2021 amma an samo shi a ranar 23 ga Mayu a kan tsohon titin Marte.

Onyeuko ya kara da cewa, dakarun da ke sintiri a Ashigashiya, Kodele da Apagaluwa a karamar hukumar Gwoza sun ci karo da 'yan ta'adda wadanda suka yi musayar wuta da su.

"'Yan ta'addan sun tsere sakamakon tsanantar wutar dakarun yayin da dakarun suka samo tumaki 40.
"Har ila yau, a ranar 31 ga watan Mayu, dakarun sun dakile wani farmakin 'yan ta'addan a Firm Base Arege a karamar hukumar Abadam ta jihar Borno kuma sun halaka 'yan ta'addan da yawa yayin da wasu suka tsere a firgice.
"Jimilla, dakarun sun samo bindiga kirar AK-47 10, AK-56 biyar, bindiga FN da sauransu.
"Hakazalika, an samo bindiga AA daya, carbon harsasai 164 da wasu 111, bindigar motar yaki daga, bindigar Shika 1, abubuwa masu fashewa biyu, injin mota daya, akwatuna hudu da injin ban ruwa daya.

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Rundunar soji ta magantu kan labarin barnar da 'yan ta'addan Kamaru suka yi a Najeriya

"Sojojin sun ceto iyalan 'yan ta'addan 100 wadanda suka hada da mata 33.
"Sun halaka 'yan ta'adda 14 tare da cafke wasu 15. An mika dukkan kayayyakin da aka samo, iyalansu da aka ceto da 'yan ta'addan da aka kama ga hukumomin da suka dace don daukar matakan da suka dace," yace.

Onyeouko yace ana cigaba da aikin tabbatar da ganin karshen 'yan ta'addan.

Borno: Jami'an MNJTF sun bindige 'yan ta'addan ISWAP 25, sun yi rashin jami'i 1

A wani labari na daban, jami'an tsaron hadin guiwa ta kasashe (MNJTF) yayin kokarin ganin karshen ta'addanci a yankin tafkin Chadi, ta na cigaba da samun nasarori kan ayyukan yaki da ta'addanci.

PRNigeria ta ruwaito cewa, dakarun jami'an tsaron hadin guiwar kasashe tare da na Operation Hadin Kai sun kai samame cikin yankin Tumbun Rago, Tumbun Dilla da alkaryar Jamina a tsakiyar tsibirin tafkin Cadi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel