Jirgin Abj-Kd: Akwai yuwuwar FG ta saki 'yan ta'addan da ke tsare don fansar fasinjoji 68

Jirgin Abj-Kd: Akwai yuwuwar FG ta saki 'yan ta'addan da ke tsare don fansar fasinjoji 68

  • Alamu na nuna cewa gwamnatin tarayya za ta saki wasu kwamandojin 'yan ta'adda da masu daukar nauyinsu domin ceto fasinjoji da aka sace
  • Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa, cinikayya ta yi nisa tsakanin 'yan ta'addan da gwamnatin tarayya wurin sakin fasinjojin jirgin Abuja zuwa Kaduna
  • A kalla fasinjoji 68 ne da suka hada da mata, kananan yara da maza magidanta ke hannun 'yan ta'addan sama da wata daya

Akwai manyan alamu da ke nuna cewa gwamnatin tarayya na iya biyan bukatun 'yan ta'addan da suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna farmaki inda suka sace sama da fasinjoji 68 a Katari, jihar Kaduna a ranar 28 Maris.

Kungiyar 'yan ta'addan ta bukaci a sako wasu daga cikin kwamandojinsu da masu daukar nauyinsu sannan su sako wadanda suka yi garkuwa da su, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Jirgin Abj-Kd: Akwai yuwuwar FG ta saki 'yan ta'addan da ke tsare don fansar fasinjoji 68
Jirgin Abj-Kd: Akwai yuwuwar FG ta saki 'yan ta'addan da ke tsare don fansar fasinjoji 68. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

A kalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 26 suka jigata yayin da 'yan bindiga suka saka bam a layin dogon kuma suka fara harbe-harbe kan jirgin da ke tafiya zuwa Kaduna.

'Yan bindigan sun sako wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su. Daga ciki akwai manajan daraktan BOA, Alwan Hassan, Sadiq Ango Abdullahi, dan shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Punch a ranar Lahadi ta gano cewa, sasanci tsakanin 'yan ta'addan da gwamnati yana cigaba. A farko gwamnatin ta fara tunanin ko ta kai farmakin karar da kowa a sansanin ne, wanda hakan ke da hatsari.

A ranar Laraba da ta gabata ne 'yan bindigan suka saki hoton jaririya mace wacce daya daga cikin matan da ke hannunsu mai juna biyu ta haifa.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

An sakankace cewa sun saki hoton jaririyar ne saboda su nuna wa duniya cewa jaririyar tana cikin koshin lafiya wanda hakan zai karfafa guiwar masu sasanci da su.

Majiyoyin tsaro sun ce 'yan bindigan sun dage kan cewa sai dai a sako mambobinsu da ke hannun hukuma tare da basu wasu kudi masu nauyi kafin su saki wadanda suka sace da suka hada da kananan yara, mata da magidantan maza.

"Sasancin da ake yi tsakanin 'yan ta'adda da gwamnati yana tafiya, amma gwamnati na duba yadda za ta karbo jama'a ne ba tare da an samu tangarda ba.
"'Yan bindigan na son a saki kwamandojinsu da masu daukar nauyinsu, suna kuma son kudi makudai. Ana sasancin da su ta yadda ba za a yi karantsaye ga tsaron kasa ba ko kuma lafiyar wadanda aka sace," majiyar tace.

Farmakin jirgin kasa: Bayan makonni 2, iyalan fasinjoji na son tattaunawa da 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Boko Haram sun sheke na kusa da Shekau bayan yunkurin mika kansa ga sojoji

A wani labari na daban, ya zama abun azabtarwa da tashin hankali ga iyalan da 'yan bindiga suka yi awon gaba da 'yan uwansu a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan da ya gabata.

Harin ya faru ne a 28 ga watan Maris a dajin Dutse cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, wanda ya lashe rayukan mutane takwas, tare da raunata wasu 26 bayan fasinjoji da dama da suka bace - wadanda ake zargin 'yan bindiga ne suka yi awon gaba da su.

Channels Tv ta ruwaito cewa, bayan sati biyu da batan su, iyalansu na sa ran za su samu 'yanci daga garkuwan da aka yi dasu, duk da sun ki amincewa da neman sasanci da 'yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng