Farmakin jirgin kasa: Bayan makonni 2, iyalan fasinjoji na son tattaunawa da 'yan bindiga

Farmakin jirgin kasa: Bayan makonni 2, iyalan fasinjoji na son tattaunawa da 'yan bindiga

  • Iyalan wadanda aka yi garkuwa dasu a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun bukaci gwamnatin tarayya da ta bude tattaunawa tsakaninta da 'yan bindigan
  • Hakan yazo ne bayan masu garkuwa da mutanen sun bayyana a wani bidiyo da ya yadu a yanar gizo suna bukatar gwamnati ta cika sharuddansu
  • Iyalan sun ba gwamnatin awanni 72 da ta dauki matakan da suka dace don tseratar da masoyansu daga kangi in ba haka ba zasu dauki matakan da suka dace

Abuja, Kaduna - Ya zama abun azabtarwa da tashin hankali ga iyalan da 'yan bindiga suka yi awon gaba da 'yan uwansu a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan da ya gabata.

Harin ya faru ne a 28 ga watan Maris a dajin Dutse cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, wanda ya lashe rayukan mutane takwas, tare da raunata wasu 26 bayan fasinjoji da dama da suka bace - wadanda ake zargin 'yan bindiga ne suka yi awon gaba da su.

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abuja-Kaduna: 'Yan ta'adda sun saki sabon bidiyon fasinjoji, suna rokon gwamnati

Farmakin jirgin kasa: Bayan makonni 2, iyalan fasinjoj na son tattaunawa da 'yan bindiga
Farmakin jirgin kasa: Bayan makonni 2, iyalan fasinjoj na son tattaunawa da 'yan bindiga. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Channels Tv ta ruwaito cewa, bayan sati biyu da batan su, iyalansu na sa ran za su samu 'yanci daga garkuwan da aka yi dasu, duk da sun ki amincewa da neman sasanci da 'yan bindigan.

Haka zalika, sun gabatar da taruka da sa ran gwamnatin za tayi wani abu akai, amma ba tare da jin kwatankwacin labarin ba har yanzu, sun fawwala lamurransu ga Ubangiji da fatan zai share musu hawayensu.

Dr Abdulfatai Jimoh, wanda ya jagoranci kungiyar 'yan uwan wadanda aka yi garkuwan dasu, ya bukaci gwamnati ta zanta da 'yan bindigan kamar yadda suka bukata a wani bidiyo da ya yadu kwanan nan.

"Masu garkuwa da mutane sun ce mu zama cikin shiri domin zasu tuntubemu, amma bamu sake ji daga garesu ba tun lokacin," a cewar Jimoh.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22

"Tun lokacin da lamarin nan ya auku, mun sa rai zuwa yanzu gwamnati, Hukumar jiragen kasan Najeriya da Ma'aikatar sufuri ta tarayya za ta nemo 'yan uwan wadanda aka yi garkuwan dasu sannan su fada mana irin kokarin da suke yi don ganin sun ceto masoyanmu ba tare da wani rauni ba."
"Maganar gaskiya, babban aikin kowacce gwamnati shi ne ta tsare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa. Mun yi imani gwamnatinmu zata iya kuma tana iyawa. Har sai bayan wasu kwanaki muna sa ran samun kira daga masu garkuwa da mutanen, saboda hakan suka yi mana alkawari bayan mun ga bidiyon, sun yi fashin baki a kan cewa su na so su yi magana da gwamnati; akwai wani abu tsakaninsu da gwamnati.
"Ba mu san me suke nema daga gwamnati ba. Amma yanzu wata dama ce kuma kafa da gwamnati za ta ceto mana masoyanmu ta hanyan bude kafar sadarwa tsakaninsu ('yan ta'adda). Hakan bai saba ka'ida ba. Ana haka a ko ina a duniya."

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Rayayyun gawawwaki?

A cewar iyalan, gwamnati ce ke da alhakin tsaresu a koda yaushe, amma hukumomi na cigaba da nuna halin ko in kula da yin kunnen uwar shegu don tabbatar da an saki masoyanmu.

Yayin da masu garkuwa da mutanen ba su riga sun bukaci kudin fansa ba, iyalan sun zauna a ranar Litinin, gami da amincewa da bawa gwamnatin tarayya kwanaki uku, kin yin hakan zai sa su yanke shawarar yadda za su ceto 'yan uwansu.

TheCable ta ruwaito cewa, 'yan uwan fasinjojin sun bada sa'o'i 72 ga gwamnati da ta ceto 'yan uwansu.

"Bamu san me ke tsakaninsu ba, amma akwai abunda zasu iya yi don kare rayukan 'yan Najeriya," a cewar Jimoh.
"Rayuwa ta yi karanci ko da kuwa rayuwar mutum daya ne.
"Muna rokon gwamnatin Najeriya da tayi duk abunda ya dace karkashin ikonta, tunda abu ne wanda bai fi karfin gwamnati ba. Muna rokonsu da su fito su bude tattaunawa tsakaninsu da 'yan bindiga don 'yan uwanmu su dawo garemu cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi

"Tsawon kwana 15 da suka shude, bama samun isashshen bacci. Muna rayuwa ne kamar gawawwaki. Mun yanke shawarar bawa gwamnati awanni 72 da su yi duk abunda ya dace don ceto mana masoyanmu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel