Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta ba da umarnin a fara bincike kan yadda dalibai suka kashe wata daliba da ta zagi Annabi
  • Wannan lamari ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta yayin da bidiyo ya yadu kan yadda lamarin ya faru
  • Bayan yin Allah wadai da batun, hukumomin tsaro sun fara bincike, tuni gwamnati ta bayyana matakin daukar hukuncin doka

Jihar Sokoto - Gwamna Aminu Tambuwal ya umurci ma’aikatar ilimin gaba da sakandare da sauran hukumomin da abin ya shafa da su fara bincike kan kashe wata dalibi a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto.

Rahotanni a baya sun rawaito cewa, an samu tashin hankali daga dalibai a kwalejin na Sokoto, biyo bayan da wani sakon sautin murya ya yadu kan yadda dalibar ta zagi Annabi Muhammadu SAW a kafar sada zumunta.

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

Daliban da suka fusata sun tarfa dalibar, inda suka kashe ta tare da kona gawarta a harabar jami’an tsaron makarantar bayan da suka yi galaba a kan jami’an tsaron makarantar da ke boye da ita.

Gwamna Tambuwal ya nemi a yi bincike kan kashe daliba a Kwaleji
Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Bayan haka, gwamnatin jihar ta ba da umarnin rufe cibiyar har abada, kana Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai da wannan aika-aika da daliban suka aikata, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi a taron manema labarai, Kwamishinan Yada Labarai na jihar Sokoto, Isa Bajini-Galadunci, ya ce Gwamna Tambuwal ya bukaci ‘yan jihar da su kwantar da hankalinsu kana su kasance masu bin doka da oda.

Ya kuma tabbatar musu da cewa za a dauki matakin da ya dace bayan binciken, inji wani rahoton jaridar Daily Nigerian.

An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

Kara karanta wannan

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

Akalla mutane biyu ne aka kama bisa laifin kashe wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta bayyana a ranar Alhamis, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar rundunar ‘yan sandan, an zargi Deborah Samuel, ‘yar matakin mataki na biyu a kwalejin, da yin wani rubutu a dandalin sada zumunta wanda ya nuna batanci ga manzon Allah (SAW).

Rundunar ‘yan sandan ta ce daliban un dauki matashiyar da karfin tsiya daga wurin jami’an tsaro da hukumomin makarantar, suka kashe ta tare da konata Kurmus.

Wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu maza suke jifanta da sanduna tana kwance a kasa sanye da kaya mai launin ja, inji rahoton Tribune Online.

Bidiyon kalaman da 'yar kwalejin ilimi a Sokoto tayi ya bayyana, Sarki Musulmi ya yi Allah-wadai

A wani labarin, mai Alfarma Sarkin Musulmi,Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi Allah-wadai bisa abinda ya auku a kwalejin ilmin Shehu Shagari dake Sokoto wanda yayi sanadiyar rashin rayuwar daliba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi

Masarautar Sarkin Musulmi a jawabin da ta saki tace:

"Masarauta ta samu labarin abin takaicin abubuwan dake faruwa a kwalejin ilmin Shehu Shagari dake Sokoto da ya kai ga mutuwar dalibar makarantar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.