Daga karshe, Shugaban Buhari ya bayyana wanda zai miƙa wa Mulki a zaɓen 2023

Daga karshe, Shugaban Buhari ya bayyana wanda zai miƙa wa Mulki a zaɓen 2023

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ƙara magana kan wanda zai iya miƙa wa ragamar mulkin Najeriya bayan zaɓen 2023
  • Da aka tambaye shi kan haka bayan kammala Sallar Idi a Abuja, Buhari yace zai miƙa mulki ga duk wanda yan Najeriya suka zaɓa
  • Ya kuma kara da kalubalantar manyan hafsoshin tsaro su bi yan ta'adda har inda suke su kawar da su daga doron duniya

Abuja - Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara matsowa kusa, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sake magana kan mutumin da zai gaje shi bayan wa'adinsa ya ƙare.

Daily Trust ta rahoto cewa a shekarar da ta gabata lokacin da ya zanta da wata kafar Talabijin a Najeriya, shugaba Buhari ya ce bai damu da ko waye zai gaji kujerarsa ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto, ya nemi a yi bincike

Daga bisani kuma shugaban ya ce duk da yana da wanda yake son ya gaje shi a zuciyarsa, amma ba ya son ya bayyana wa duniya shi saboda, "da yuwuwar a kawar da shi idan ya faɗa."

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Hoto: Buhari Sallau/facebook
Daga karshe, Shugaban Buhari ya bayyana wanda zai miƙa wa Mulki a zaɓen 2023
Asali: Facebook

Sai ɗai da yake jawabi bayan kammala Sallar Idin ƙaramar Sallah a Barikin Mambila dake Abuja, Buhari ya jaddada jajircewar da gwamnatinsa ke yi na tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka tambaye shi kan wanda yake son ya miƙa wa mulki a 2023, Shugaba Buhari ya ce: "Mutumin da yan Najeriya suka zaɓa."

Shugaba Buhari ya kalubalanci Hafsoshin tsaro

Bayan haka shugaba Buhari ya ƙalubalanci hafsoshin tsaro da dukkan hukumomin tsaron ƙasar nan su bi yan ta'adda har maɓoya su kawar da su daga duniya.

Buhari ya jaddada manufar gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana domin dawo da zaman lafiya a tsakanin yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Ya ƙara da cewa wajibi a tabbatar da tsaron manoma yayin da suke gab da komawa gona, domin ceto ɓangaren samar da abincin ƙasar nan.

Tribune Online ta rahoto Buhari na cewa:

"Zamu cigaba da samar da tsaro musamman lokacin da muke fuskantar damina, saboda manoma su koma gonakin su, har Allah ya sa mu fita daga hatsarin tsaron abinci."
"Shugabannin dakarun tsaro; na sojojin ƙasa, Sojojin ruwa, sojojin sama, Sufetan yan sanda da sauran makamantansu sun san halin da ake ciki sarai. Haƙƙin su ne binciko inda yan ta'adda suke kuma su sheƙe su."

A wani labarin kuma Wani Fitaccen ɗan kasuwa ya fito takara a NNPP, ya shirya fafatawa da Sanata Kwankwaso

Fitaccen ɗan kasuwa masani a harkokin msana'antu, Olufemi Ajadi, ya ayyana tsayawa takara karkashin jam'iyyar NNPP.

Hakan na nufin ɗan takarar zai gwabza da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso a zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Asali: Legit.ng

Online view pixel