Yanzu-Yanzu: Ministan Kwadugo, Chris Ngige, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2023

Yanzu-Yanzu: Ministan Kwadugo, Chris Ngige, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Bayan gana wa da shugaba Buhari, Ministan Kwadugo, Chris Ngige, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa
  • A wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu, Ngige ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari da kuma neman shawari wurin makusanta
  • A cewarsa hakan zai ba shi cikakkiyar damar maida hankali kan aikinsa da taimaka wa shugaban kasa

Abuja - Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 dake tafe.

TVC ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Ministan, kuma da kwanan watan Jumu'a 13 ga watan Mayu, 2022.

Dakta Ngige ya ce ya yanke wannan shawarin ne bayan gana wa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da neman shawarin iyalai, masoya da masu fatan Alheri.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Ngige ya janye daga takara.
Yanzu-Yanzu: Ministan Kwadugo, Chris Ngige, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

A sanarwan, ministan ya ce tuni ya sanar shugaban ƙasa da Sakataren gwamnatin tarayya matakin janyewarsa daga takara.

Ngige ya ce:

"Bayan faɗaɗa neman shawari da iyalai, mutanen mazaɓa, masoya da masu fatan Alheri, ina mai sanar da janyewa daga takara da neman ofishin shugaban ƙasa a zaɓen 2023."
"Sakamakon haka ba zan shiga harkokin jam'iyya da suka shafi zaɓen nan ba tun daga zaɓen fidda gwani. Na ɗauki wannan matakin ne na farko domin ƙasa ta, na samu damar maida hankali kan aiki na da taimaka wa shugaba."
"Da wannan sanarwan ina mai sanarwa mutanen mazaɓa ta, abokanan siyasa da masu fatan Alheri matakin da na ɗauka na ƙarshe."

Yaushe ministan ya shiga takara?

A ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, 2022, Ngige ya bayyana wa duniya kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa bayan shugaba Buhari ya kammala wa'adinsa a 2023.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Ya ce ya shiga takara ne biyo bayan matsin lamba daga mazaɓarsa, abokan siyasa da wasu manyan yan Najeriya waɗan da ke ganin kwarewarsa ta kai ya ɗare kujera lamba ɗaya.

A wani labarin kuma Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya bayyana sunan ɗan takarar da yake rokon Allah ya gaji Buhari a 2023

Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya nuna goyon bayansa ga Yemi Osinbajo a zaɓen 2023.

Malamin ya ce ya jima ya na wa mataimakin shugaban Addu'a don haka zai nunka rokon Allah ya samu nasara a zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel