2023: An samu ɗan takarar shugaban kasa da zai gwabza da Kwankwaso a NNPP

2023: An samu ɗan takarar shugaban kasa da zai gwabza da Kwankwaso a NNPP

  • Fitaccen ɗan kasuwa masani a harkokin msana'antu, Olufemi Ajadi, ya ayyana tsayawa takara karkashin jam'iyyar NNPP
  • Hakan na nufin ɗan takarar zai gwabza da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso a zaben fidda gwani
  • Ya yi kira ga matasa sun fito kwansu da kwarkwata domin lokaci ya yi da zasu kawo canjin da suke mafarkin kawowa Najeriya

Abuja - Masanin harkokin masana'antu, Olufemi Ajadi, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP.

Ajadi, shugaban masana'antar haɗa kayan sha, Bullion Neat Global, ya bayyana aniyarsa a Sakatariyar NNPP ta ƙasa dake Abuja ranar Alhamis.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da aka aike wa jaridar Punch ranar Jumu'a, 29 ga watan Afrilu, 2022.

Jam'iyyar NNPP.
2023: An samu ɗan takarar shugaban kasa da zai gwabza da Kwankwaso a NNPP Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Yayin da yake ayyana tsayawa takarar kujera lamba ɗaya, Ajaɗi, ya yi alƙawari samar da tsayayyun ofisoshin siyasa a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Shugaban APC ya yi tsokaci kan yankin da zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023

Ya ce:

"Wannan ce jam'iyya ɗaya tilo da take da manufa da Agenda irin wacce muke ta yawon nema, ita ce jam'iyyar da ta tara matasan Najeriya waɗan da nake wakilta, da kuma sauran yan Najeriya."
"NNPP ce kaɗai jam'iyyar da zata share mana fage da kowane ɗan Najeriya daga kowane sashi zai sha romon demokaraɗiyya."
"Saboda haka, ina kira ga matasan Najeriya su shirya su ɗaura ɗamara, lokaci ya yi da zamu kawo canjin da muke fatan gani a ƙasar mu."

Ya yi magana kan Kwankwaso

Haka zalika, Ajadi ya yi amfani da wannan dama wajen kira da nuna ladabi ga abokan takararsa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sunday Oginni wanda ke neman takarar gwamna.

A wani labarin kuma Jerin Sunayen gwamnonin APC, PDP da suka shirya janye wa Jonathan takarar shugaban ƙasa a 2023

Kara karanta wannan

2023: Sabon ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayyana aniyarsa a APC, ya nemi a rage masa kuɗin Fom

Wasu fitattun yan siyasa sun shirya canza kudirinsu na neman takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Wasu gwamnoni biyu masu ci sun yanke cewa zasu iya janye wa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel